Gwamnatin Barno da bankin masana’antu za su tallafawa masu kananan sana’o’I a jihar

0

Gwamnatin jihar Barno da bankin masana’antu BOI sun hada hannu domin tallafa wa kananan masana’antun dake jihar da jari.

Babagana Zulum da shugaban sashen tallafa wa kananan masana’antu na bankin Shekarau Umar suka saka hannu a takardan yarjejeniyar.

A wannan takarda gwamnatin jihar Barno da banki za su samar da Naira biliyan daya domin tallafawa kananan masana’antu dake bukatan tallafi a kananan hukumomi bakwai na jihar.

Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin yada labarai Isa Gusau ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai.

Gusau ya ce gwamnati za ta fara tallafawa masu kananan sana’o’I dake kasuwan Monday,kasuwan Gamboru, Tashan Baga, ‘yan itace, da masu siyar da kayan lambu.

Daga nan kuma sai wadanda ke kananan hukumomin Biu, Ngala, Monguno, Dikwa, Bama and Gwoza.

Idan ba a manta ba a watan Disemba 2019 gwamna Babagana Zulum ya nemi bankin BOI ta tallafa wa kananan masana’antun dake jihar domin inganta rayuwar mutanen da aiyukkan Boko Haram ta shafa a jihar.

Share.

game da Author