An bankado gidan da ake tara mata kanana ana yi musu ciki, idan suka haihu a saida jariran

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta gano wani gidan da ake tara mata ana dirka musu ciki bayan sun haihu sai a siyar da jariran a kauyen Imedu Olori dake karamar hukumar Obafemi Owode.

Kakakin rundunar Abimbola Oyeyede ya sanar da haka a garin Akure ranar Alhamis.

Ya ce sun gano wannan wuri ne a dalilin karan da daya daga cikin matan da ake tarawa a gidan ta kawo musu bayan ta gudu daga gidan.

Oyeyede ya ce matar ta bayyana cewa ta tsinci kanta ne a wannan gida bayan mai wurin Mrs Ogbonna ta rude ta shiga gidan.

Yarinyar ta ce Mrs Ogbonna na kawo maza cikin gidan su kwana da ‘yan matan. Idan suka yi ciki suka haihu sai matan ta dauke jariran ta siyar.

Oyeyede ya ce sun ceto mata 12, wasu shida na dauke da tsohon ciki wanda shekarun su bai wuce 20 zuwa 25 ba daga wannan gida.

Ya kuma ce sun kama Florence Ogbonna, Chibuke Akabueze da Chibuzor Okafor dake da hannu a harkokin gidan.

Idan ba a manta ba a watan Satumba 2019 ne rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos, ta bayyana ceto wasu ‘yan mata su 19, kowace dauke da ciki a wani gidan da ake tara mata ana dirka musu ciki, bayan sun haihu a sayar da jira-jiran.

Rundunar ta gano gidan a unguwar Iyawale, cikin yankin Ikotun. Ya kara da cewa matan sun kama daga shekaru 15 zuwa 28.

Share.

game da Author