Kasar Kamaru ta killace mutum na farko da aka yi wa gwaji aka gano ya kamu da cutar coronavirus.
Mutumin wanda dan asalin kasar Fransa ya tsallako kasar ne inda na’urar gwaji ya nuna yana dauke da cutar.
Ministan kiwon lafiyar kasar, Malachie Manaouda ya bayyana cewa tuni dai har an killace wannan bafaranse a babban asibiti dake Yawonde.
Cutar coronavirus ya na ci gaba da yaduwa a nahiyar Afrika inda wasu mutane 7 suka kamu a kasar Aljeriya.
Yawan wadanda suka kamu yakai mutum 17 kenan a kasar.
Haka kuma kasar Senegal itama an samu mutum hudu da suka kamu da cutar. Ita ma kasar Afrika ta kudu an gwada wani da aka tabbatar ya kamu da cutar. Baya ga kasar Masar da ita ce kasa ta farko da cutar ya fara bayyana a nahiyar Afrika din.
Zuwa yanzu dai akalla sama da mutane 100,000 ne suka kamu da cutar, sannan sama da mutane 3000sun rasu.