Gwamnatin jihar Filato ta sanar cewa ta kammala shiri tsaf don bude asibitin gwajin cutar coronavirus a jihar.
Gwamnan jihar Simon Lalong ya sanar da haka a zaman da ya yi da shugabannin majalisar dokokin jihar da kwamitin da gwamnan ya kafa domin dakile yaduwar cutar, da shugabannin jam’iyyar APC dake jihar da aka yi a fadar gwamnati a garin Jos.
Lalong ya ce an yi wannan zama ne domin tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar a jihar.
“A yanzu dai cutar bai shigo jihar Filato ba kuma haka muke sa rai in Allah ya yarda. Amma hakan zai tabbata ne idan muka hada hannu wajen kiyaye matakan hana yaduwar cutar da gwamnati za ta kafa.
Kakakin majalisar dokoki Ayuba Abok ya jinjina matakan hana yiwuwar cutar da gwamnati ta dauka.
Sannan shugaban jam’iyyar APC Letep Dabang ya yi kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen wayar da kan mutane game da cutar musamman mazauna karkara.
Sakataren gwamnati Danladi Atu, ya ce gwamnati ta bude asusu domin mutane su bada gudunmawa.
Mutane 135 ne ke dauke da cutar, 8 sun warke sannan biyu sun mutu a Najeriya.
Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.
A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya ranar lahadi ya ce gwamnati ta saka dokar garkame garin Abuja da Legas na makonni biyu har sai an kammala yin gwajin wadanda ake zargin sun kamu da cutar.
Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.
Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukumar NCDC.