Ba a bukatan karin na’urar ba da iska a Najeriya – Minista

0

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa Najeriya ba za ta bukaci karin na’urar ba da iska ba a asibitoci domin kula da wadannan suka kamu da cutar coronavirus.

Ehanire ya fadi haka ne ranar Litini a Abuja da yake ansa tambayoyi daga wajen manema labarai.

Ya ce tabbas babu isassun na’urar ba da iska a kasar nan amma ma’aikatar ta tsara hanyoyin da za su taimaka wajen samar da na’urar da ake dasu zuwa asibitocin da ake bukata.

Na’urar ba da iska na’ura ce dake taimaka wa wanda ya kamu da coronavirus iya yin mumfashi yadda ya kamata.

Ministan ya ce a yanzu dai mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya basu bukatan wannan na’ura domin a kwanakin baya mutum daya ne aka yi masa amfani da shi a asibiti.

Ya ce babu kasan da bata fama da rashin isassun na’urar ba da iska ba. Da yawa ana ta kara yin su ne

“Ba na’uran ba da iska ne ke warkar da mutum ba amma zuwa asibiti domin yin gwajin cutar ne yafi dacewa.”.

A yanzu dai mutane 135 nesuka kamu da coronavirus a kasar nan, 8 sun warke sannan biyu sun mutu.

Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.

A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya ranar lahadi ya ce gwamnati ta saka dokar garkame garin Abuja da Legas na makonni biyu har sai an kammala yin gwajin wadanda ake zargin sun kamu da cutar.

Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.

Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukumar

Share.

game da Author