Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo ya yi kira ga dukkan kamfanonin layikan waya da suka hada da MTN, Glo, Airtel, 9Mobile su yi wa jama’a watandar buga waya kyauta a layikan su, domin rage musu kuncin zaman gida a wannan mawuyacin halin zaman-dirshan domin kauce wa Coronavirus.
Keyamo ya ce idan suka yi haka, mutane masu yawan gaske zasu samu saukin sadarwa tsakanin junan su, kasancewa harkoki sun tsaya cak, kowa na zaune a gida.
Ya kuma roke su su zuba wa dukkan kwastomin na su kyautar data, wacce ake amfani da ita wajen sada zumunta tsakanin jama’a a soshiyal midiya.
Haka kuma Minista Keyamo ya roki kamfanonin DSTV da Star Times, su saukake wa dukkan masu kallon tashoshin talbijin a karkashin tsarin su biyan kudin wata daya cur. Wannan inji shi wani hobbasa ne kuma babbar gudummawa ce za su bayar don dakile Coronavirus daga kasar nan.
Ministan ya yi wannan kira ranar Litinin a shafin sa na Twitter, inda ya kara yin nuni da cewa a matsayin sa na ministan da aka kallafa wa kula da ma’aikata da jin dadin su, ya san idan aka yi wannan kokarin, to za a taimaka wa mutane da yawa runda garuruwa da dama zirga-zirga ta tsaya cak.