Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta dauki wasu matakan da za su taimaka wajen samar wa sojoji da iyalen su kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus.
Rundunar ta ce za ta kakkafa wuare a barikin sojoji da duk wuraren da sojoji ke zama da mu’amula domin hana yaduwar cutar.
Darektan yadda labarai na rundunar Onyema Nwchukwu ya shaida wa PREMIUMTIMES haka ranar Asabar yana mai cewa rundunar ta yi haka ne bayan da aka samu sanarwar tabbacin bullowar cutar a jikin wani dan kasar Italy ranar 27 ga watan Fabrairu.
“ An killace wannan mutum a wani asibiti na musamman.”
Nwachukwu yace ma’aikatan kiwon lafiya za su sa ido kan duk marasa lafiyan dake kwance a asibitocin su domin gano alamun cutar.
“Za kuma mu wayar da kan duk ma’aikatan mu da iyalansu kan hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar sannan kuma mun ajiye man tsaftace hannu “Hand Sanitizer’ a duk ofisoshin mu domin ma’aikata su rika amfani da shi.
Bayan haka ministan kiwon lafiya Osagie Ehnaire ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankulan su yana mai cewa gwamnati ta yi tanadin da zai taimaka wajen hana yaduwar cutar a kasar nan.
Ya kuma ce gwamnatin Najeriya ba za ta hana mutane da baki shiga da fita kasar nan ba sannan gwamnati ta fara gudanar da bincike domin gano ko akwai mutanen da suka kamu da cutar a dalilin yin mu’amula da dan kasar Italy a jihohin Legas da Ondo.
Daga nan ma hukumar hana yaduwar cututtuka ta yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar da hukumar ta bada.
HANYOYIN SAMUN KARIYA DAGA CUTAR:
1. Yawaita wanke hannu da ruwa da sabullu ko kuma da man tsaftace hannu ‘Hand Sanitizer’ idan babu ruwa.
2. A rika tsaftace muhalli.
3. Idan za a yi tari ko kuma atishawa a yi amfani da tsumma domin kare baki da hanci.
4. A guji yawan kusantan mai fama da mura ko kuma alamomin cutar.
5. Wurarren aiki su tabbatar sun ajiye ruwa da sabullu domin ma’aikata su rika wannke hannu ko kuma a ajiye man tsaftace hannu.
6. A guji shan magani ba tare da izinin likita ba.
7. Gaggauta zuwa asibiti na cikin hanyoyin da zai taimaka wajen warkar da cutar a jikin mutu.
8. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun kare kansu yayin da suke gudanar da aiyukkansu.
9. Za a iya kiran wannan lambar 07032864444 a duk lokacin da ba a ji daidai ba a jiki.