Yadda ‘Yan bindiga suka bindige mutane 50 a Kaduna

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki ya yanku hudu da ke karkashin Karamar Hukumar Igabi, har suka kashe mutane 50.

Sun kai wannan mummunan farmakin ne a kauyukan Kerewa, Zareyawa da Marina, dukkan su a cikin Mazabar Kerawa.

Kafafen yada labarai sun tabbatar da cewa an kai farmakin ne wajen karfe 6 na safiyar Lahadi, daidai lokacin da ba a dade da gama sallar asubahi ba.

An ce maharan ba su bar babba ko yaro ba, hatta jira-jirai sabuwar haihuwa da almajirai sai da suka kashe.

Mazauna kauyukan sun rika tserewa, yayin da ake harbin su. An kuma banka wa gidaje masu tarin yawa wuta, kuma an saci kayan abinci.

Kansilan Mazabar Ketawa, Dayyabu Kerawa ya shaida cewa mutum 51 aka kashe, kuma babu wanda ya san za su kai hare-haren, sai dai kawai aka gan su.

An kasa samun lambar kakakin yada labarai na ‘yan sandan Jihar Kaduna. Haka shi ma Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Samuel Aruwan, ba a samu lambar sa ba.

Amma daga baya kakakin ‘yan sanda ya tabbatar wa manema labarai cewa an kai harin.

Cikin 2019 garuruwan cikin Kananan Hukumomin Kajuru, Giwa da Igabi sun sha fama fa hare-haren ‘yan bindiga.

Sun taba sanar da mazauna wasu kauyukan Igabi cewa su tashi ko su far musu. Hakan ta sa tilas dubban jama’a suka yi Laura zuwa Birnin Yero, inda suka yi mafaka cikin ajujuwan firamaren garin.

Share.

game da Author