Mai Shari’a na Kotun Yanki (Area Court) a Gombe, ya tura wasu ‘yan siyasa masu adawa da Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe zuwa kurkuku.
Sai dai kuma abin da ya daure wa mutane kai shi ne yadda ‘yan sanda suka gurfanar da su a kotu, da kuma yadda alkalin ya yi zaman sauraren shari’ar ta su a ranar da aka ce kada kowace kotu ta yi aiki a Jihar Gombe.
‘Yan sanda sun kama wani tsohon Hadimin Tsohon Gwamna Ibrahim Dankwambo, mai suna Boza-boza, a bisa zargin ya ci mutuncin Gwamna Inuwa Yahaya.
Wannan kamu da aka yi wa Boza-boza tare da abokin sa Adamu Babale, ya sa Jihar Gombe ta shiga sahun jihohin da ake garkame masu adawa da gwamna a soshiyal midiya.
Watannin baya PREMIUM TIMES ta yi cikakken rahoton kan jihohin da gwamnonin su ba su da jimirin suka daga bakin masu adawa a soshiyal midiya.
Bayan an kama Boza-boza an kulle a Ofishin ‘Yan Sanda na Pantami, sai abokin sa mai suna Adamu Babale ya je belin sa. Maimakon a ba shi beli, sai shi ma aka damke shi.
‘Yan sanda sun zarge su da laifin “kokarin zagin wani mai suna Inuwa Yahaya.” Daga nan an daure da ankwa, aka tasa keyar su zuwa kotu.
Duk da cewa Kwamishinan Shari’a na Jihar Gombe, Mu’azu Pindiga ya bada hutu ga dukkan kotina da alkalan kasar, hakan bai hana alkalin fitowa kotu ba, domin ya yi hukunci a kan batun. Ya kuma tura su kurkuku take.
Kakakin Gwamnan Gombe Abdullahi Misili_ya nesanta Gwamna Yahaya daga kamun da aka yi musu.
Ana tuhumar Boza-boza saboda ya kira Inuwa “Shugaban marasa cika alkawari.”
Discussion about this post