CORONAVIRUS: Najeriya ta yi wa sama da mutum 2,000 gwaji, yanzu ana farautar mutum 6,000

0

Najeriya ta gudanar da gwajin cutar Coronavirus a kan mutum sama da 2,000. Amma wadanda aka samu na dauke da cutar ba su kai kashi 10% bisa 100% ba.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana haka, tare da cewa NCDC na neman wasu mutane sama da 6,000 da aka tabbatar sun cakudu da wasu da suka kamu da cutar.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda zuwa ranar Juma’a dai an tabbatar da kamuwar mutum 111 suka kamu.

Ihekweazu ya yi magana ta gidan talbijin na Channels, awoyi da dama bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya Jawabin matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka.

Ya zuwa yau jihar Legas an samu mutum 68 a Lagos,21 a Abuja, Ogun mutum 3. Sauran jihohi irin su Ekiti, Osun, Enugu, Bauchi, Benuwai da Kaduna duk samu bullar cutar.

Jim kadan bayan jawabin Buhari, Ministan Lafiya ya bayyana cewa an killace jama’a ne a Lagos, Ogun da Abuja domin a samu saukin cigaba da farautar duk wani da aka san ya yi mu’amalar kusanci da wadanda suka kamu da cutar.

Daga nan ya ce akwai ayyuka da yawan gaske a karkashin NCDC, kuma har yau duniya ba ta da masaniyar takamaimen wannan cuta wadda ta yi sanadiyyar mutuwar dubban jama’a a duniya.

Ya yi gargadin cewa nasarar da NCDC za ta iya samu wajen dakile Coronavirus ta dogara ne kacokan a kan irin hadin kai da goyon bayan da jama’a suka bayar wajen daukar matakan duk da aka umarce su su bi, musamman killace kai a gida da kuma kula da tsafta.

Share.

game da Author