A jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ranar Lahadi ya jero wasu matakai da gwamnati ta dauka domin dakile yaduwar cutar coronavirus a Najeriya.
Ga matakan:
1. Mu a na nan Najeriya, matakai guda biyu ne mu ke dauka.
2. Na farko shi ne kare rayukan ‘yan Najeriya da sauran mazauna cikin kassr, sai kuma dukkan wuraren aiki, kasuwanci da neman abinci a wanann mawuyacin halin rike nauyin kula da iyali.
3. A yau mun shigo da tsauraran matakai, cikin su har da rufe hanyoyin shigowa cikin kasar nan da sauran matakai.
4. Wasu daga matakan da muka dauka za su takura wa jama’a. Amma dai wannan mataki ne na sadaukarwa domin mu gudu tare mu tsira tare
5. A kokarin da Najeriya ke yi wajen yaki da Coronavirus, ba a maganar azarbabi ko batun jan-kafa. Sai dai batun yin dukkan abin da ya dace, wadan hukumomin da suka dace ke gudanarwa tare da kwararrun jami’ai,
6. Za mu ci gaba dogaro da shawarwarin da Ma’aikatar Kula da Lafiya, NCDC da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki ke bayarwa a wannan mawuyacin halin da muka tsinci kan mu a ciki.
7. Don haka ina kira ga kowa ya rika kiyayewa da ka’idojin da za su rika gindagaya akai-akai.
8. Kamar yadda kowa ya sani, Legas da Abuja ne wannan cuta ta fi watsuwa. A yanzu za mu fi bayar da fifiko ne wajen hana cutar fantsama daga wadanan birane biyu zuwa sauran garuruwan kasar nan. Sauran garuruwa da yankunan ma ta zu yi dukkan abin da ya dace don hana cutar bulla da fantsama.
9. Dalili kenan mu ka fitar da naira bilyan 11 a tashin farko domin yin duk yadda yadda yadda za mu Yi mu hana cutar fantsama sauran jihohi
10. Mun kuma kafa Kwamitin Shugaban Kasa mau hana Coronavirus fantsama. Ya na ci gabada aiki, tare da bayar da rahoto a kowace rana.
11. Kudirin mu shi ne mu tabbatar kowace jiha ta samu goyon baya da ma’aikata da gaggawa.
12. A Legas da Abuja mun dauki daruruwan ma’aikatan da za su yi aiki a wuraren tuntuba da kuma wajen kokarin gano wadanda suka kamu da cutar da kuma ayyukan gwaji.
13. Na kuma umarci dukkan gwamnoni su dauki ma’aikatan wucin-gadi wadanda jami’an Hukumar NCDC da Geamnatin Jihar Lagos za su yi wa horon matakan shawo kan bullar cutar zuwa sauran jihohi.
14. Wannan bayar da horo zai kunshi har da wakilai daga sojojin mu da sauran bangarorin tsaro da kowane zai bayar da jami’an fannin lafiyar su.
15. A matsayin mu na kasa daya, zai kasance dukkan ayyukan da muke yi ya tafi a cikin tsari, bisa tsarin bai-daya tare da aiki da kwarewa da gogaggu a kan ka’ida.
16. Kamar yadda na fada tun farko dukkan wadanda suka kamu na samun kulawar da ta kamata.
17. Hukumomin mu na ta kokarin gano wadanda duk suka cakudu da wadanda suka rigaya suka kamu.
18. Sauran kalilan din da suka kamu a wasu garuruwa banda Lagos da Abuja kuwa, duk samu cutar ne daga wadanda suka yi tafiye-tafiye daga Lagos da Abuja din.
19. Shi ya sa mu ke ta kokarin ganin mu hana zirga-zirga tsakanin jihohi da kuma cikin kowace jiha, domin hana cutar kara fantsama.
20. Daga karfe 11 na daren ranar Litinin, 30 Ga Maris, ina sanar da cewa na hana zirga-zirga a Lagos da Abuja har tsawon kwanaki 14. Ba shiga kuma ba fita. Kowa ya killace kan sa a gida. Wannan doka ta shafi jihar Ogun, saboda kusancin ta da Lagos da kuma yawan zirga-zirga da ke gudana tsakanin jihohin biyu.
21. Duk mazauna wadannan jihohi da yankuna kowa ya zauna a cikin gida. A dakatar da fita ko tafiya wasu garuruwa. Kuma a rufe duk wani ofis ko wuraren hada-hadar kasuwanci a cikin wadannan yankuna da aka lissafa.
22. Tuni aka sanar da Gwamnonin wadannan jihohi da kuma Ministan Abuja tare da Shugabannin Tsaro da ke ko’ina wannan mataki da muka dauka.
23. Za mu yi amfani da wadannan kwanaki domin ganowa da kuma killace duk wani da aka tabbatar ya cakudu da wani wanda ya kamu da cutar. Za mu kuma tabbatar da an bada cikakkiyar kulawa ga dukkan wadanda suka kamu, sai kuma tabbatar da cutar ba ta fantsama sauran jihohi ba.
24. Amma wannan doka ba ta shafi asibitoci, likitoci da sauran jami’an lafiya da dukkan masu sarrafawa ko masana’antun samar da kayan lafiya da masu jigilar kayayyakin.
25. Akwai masu sana’o:in yau da kullum da suka hada da: kamfanonin sarrafa kayan abinci, masu raba man ferur manya da kanana, kamfanonin wutar lantarki da jami’an tsaro masu aiki a kamfanonin masu zaman kan su, duk wanann doka ba ta shafe su ba.
26. Duk da cewa dokar ba ta shafe su ba, za a rika kula da yadda suke ayyukan su, kuma za a takaita zirga-zirgar su.
27. Za a bar ma’aikatan kamfanonin wayoyin sadarwa da na gidajen radiyo, talbijin da jaridu su fita aiki, muddin suka tabbatar da cewa ba za su iya gudanar da aikin su daga gida ba.
28. Tashoshin jiragen ruwan Lagos za su ci gaba da aiki, a bisa tsari da sharuddan da aka gindaya musu. Su kuma direbobin motoci da jiragen ruwa masu jigilar kayayyakin daga tashoshin duk jami’an lafiya za su rika auna su kafin su nausa zuwa wuraren da za su kai kaya.
29. Za a rika bincike da tantance dukkan motoci da za su rika daukar kayan abinci da kayan agaji zuwa garuruwan da aka hana zirga-zirga, kafin a bari su shiga garuruwan.
30. Na umarci Ministan Harkokin Lafiya ya karkasa jami’an kula da lafiya da ke tashoshin ruwa da filayen jiragen sama, zuwa kan titinan yankunan da aka hana zirga-zirga a can.
31. Daya yau an hana zirga-zirgar jiragen sama masu daukar fasinjoji ko na daidaikun mutane har sai wanda aka bai wa izni na musamman saboda wasu dalilai na musamman na gaggawa.
32. Mu na sane da cewa dokokin nan sun yi tsauri da yawa. To amma sun zama tilas domin batu ne na ceton rayuka, musamman idan aka yi la’akari da yadda Coronavirus ta kashe dimbin jama’a a Italy, Faransa da Spain.
33. Amma dai tilas mu kalli wannan aiki da cewa wani kishin kasa ne mu ke yi domin dakilewa, magancewa da hana cutar fantsama. Don haka ina kira ga kowa da ya daina runanin zaman more rayuwa a yanzu. Ya tashi tsaye ya kare kan sa da sauran al’umma. Za mu iya galaba kan wannan cuta ce idan muka rika kiyayewa da bin dokokin da masana kimiyya da likitoci suka gindaya mana.
34. Yayin da muka shirya tsaf domin fara aiwatar da wadanan dokoki, ya kamata mu kalle su a matsayin ta mu gudummawar wajen yaki da cutar Coronavirus. Kasashe da yawa sun kafa tsauraran dokokin da suka fi na mu matsatsi da takuwarawa domin dakile wannan cuta. Kuma sun samu nasara sosai.
35. Za mu samar da kayan agaji ga mazauna kananan garuruwan da ke kewaye da Lagos da Abuja domin saukake musu kuncin rayuwar da za su shiga nan da makonni kadan.
36. Duk da cewa makarantu duk su na rufe, na umarci Ma’aikatar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma ta hada kai da Gwamnatocin Jihohi domin tabbatar da cewa ayyukan ciyar da dalibai bai samu tawaya ba a cikin wannan mawuyacin hali.
37. Na bada umarni wadanda suka karbi lamunin TraderMoni, Market Moni da FarmerMoni duk su jinkirta biyan tsawon na watanni uku.
38. Na kuma bada wannan umarnin jinkirta biya ga wadanda suka karbi basussukan Gwamnatin Tarayya a karkashin Bankin Bunkasa Masana’antu, Bankin Raya Manoma da Bankin Nexim.
39. Su ma wadanda suka karbo lamuni daga manyan cibiyoyin hada-hadar kudade na duniya, na umarci wadanda kulawa ke hannun su day su tsara yadda za a daga musu kafa, domin wadanda suka ramci kudaden su su samu saukin kuncin wannan mawuyacin halin da muke ciki.
40. Marasa galihun da ake tura wa kudaden rage radadin talauci, su ma na bada umarnin a gaggauta tura musu kudaden watanni biyu kai-tsaye a asusun bankin kowanen su. Haka mazauna sansanonin gudun hijira, su ma na bada umarnin a ba su tallafin abincin wata biyu.
41. Mu na kuma yin kira ga dukkan mai hali ya taimaki marasa halin da ke kusanci ki makwautaka da shi.
42. Yayin da mu ke addu’ar cin nasarorin dukkan abin da muka sa a gaba, to kuma mu ci gaba da shirin duk wani abu da ka iya biyo baya.
43. Dalili kenan na bada umarnin duk wani filin wasa na Gwamnatin Tarayya da Hukumomin Alhazai a maida su wuraren killace mutane da kuma asibitin wucin-gadi.
44. Ya ku ‘yan Najeriya, a matsayin mu na gwamnati za mu yi amfani da dukkan abin da ya wajaba domin ganin wadanda suka kamu sun warke. Mun kuma tsaya ka’in da na’in wajen daukar duk wani mataki daya dace domin dakile Coronavirus baki daya kasar nan.
45. Mu na farin cikin ganin yadda wasu kamfanoni da daidaikun mutane suka bayar da ta su gudummawa. Haka abokan huldar kasuwancin mu da suka yunkuro, su ma sun cancanci yabo.
46. A wanan lokacin na ke yin kira cewa a taskace dukkan kudaden agaji da gudummawar da aka samu ko ake kan samu a cikin asusu daya. Kwamitin Shugaban Kasa na Coronavirus shi ne mai hakkin tara wadannan kudade.
47. Ina so na tabbatar muku cewa dukkan wata Ma’aikata, Hukuma, Cibiya ko Bangare mai rawar takawa a a wannan hali, ya na bakin kimarin ganin an dakile wannan annoba.
48. Kowace kasa na fuskantar wannan kalubale. Amma kuma mun ga yadda wasu ‘yan kasashen suka hada kaiwajen rage yaduwar wannan cuta.
49. Ina mai sake umartar ku da ku bi ka’idojin da aka gindaya, ku goya wa Gwamnati baya da kuma marasa galihu a cikin ku.
50. Zan yi amfani da wannan dama na gode wa dukkan jami’an kula da lafiya da sauran ma’aikatan da ke bakin fama da suka sadaukar da kan su wajen ganin an yi galabar korar Coronavirus.
Discussion about this post