Sakamakon yadda cutar Coronavirus ta barke a duniya, a nan Najeriya gwamnati na ta fadi-tashin yadda za a tara makudan kudade, har naira bilyan 120 domin yakar cutar.
Neman wadannan makudan kudade kuwa ya zama tilas ga gwamnati, ganin yadda rashin kudi ya addabe ta, tun bayan faduwar farashin danyen man fetur kasa warwas.
Sannan kuma wannan karyewar farashin danyen mai ya shafi kasafin kudi na 2020.
Wannan ne ya sa aka kafa kwamiti domin tara kudaden, wanda ya kunshi iri su Aliko Dangote, Femi Otedola, Jim Ovia, Tony Elumelu, Segun Agbaje, Abdulsamad Rabiu a matsayin mambobin kwamiti.
Akalla kowanen su ya yi alkawarin tallafawa da naira bilyan 1.
A na su bangare, ministocin Najeriya sun sadaukar da rabin albashin kowanen su na watan Maris wajen kokarin dakile Coronavirus.
Kafin sannan, dan majalisar tarayya Mansur Soro daga jihar Bauchi,ya roki sauran da su tallafa da albashin su na watan Maris, domin a sayi na’urar shakar numfashi, wadda ya ce ta ki matukar karanci a jihohi 36 na kasar nan.
‘Yan Najeriya sun fusata a shafukan Twitter bayan jin labarin cewa za a fara raba wa ‘yan majalisun dankara-dankaran motoci na alfarma.
Abinda Wasu Kasashen Ke Yi
Cikin watan Fabrairu Mataimakin Firayi Ministan Singapore, Heng Swee Keat, ya bada sanarwar cewa dukkan shugabannin kasar masu rike da mukaman siyasa, ciki har da Shugaban Kasa da Firayi Minista, za su bada tallafin gaba dayan albashin su na wata daya ga yakar cutar Coronavirus.
Sannan kuma an bada alawus na musamman ga jami’an lafiya wadanda ke a sahun gaba wajen fafutikar kasar da cutar da kuma kula da wadanda cutar ta kwantar.
Kwana kadan sai kasar Hong Kong ta yi sanarwa makamanciyar wannan. Ita ma har alawus na kashi 20 na albashi ta kara wa jami’an lafiyar ta.
Su ma na kasar Morocco sun yi sanarwar tallafawa da albashin su ga Gidauniyar Sarki Mohammed’ domin yaki da cutar Coronavirus.
Daga nan kuma sai Shugaba Uhuru Kenyeta na kasar Kenya su ma suka bayyana cewa sun sadaukar da wasu kaso na albashin su.
Kenyatta da Mataimakin sa sun bayar da kashi 80 na albashin su. Akwai sauran manyan jami’an Gwamnatin Kenya da zuka sadaukar da kashi 30, wasu kuma kashi 29 na albashin su.
Haka su ma ‘yan Majalisar Pakistan ba a bar su a baya ba wajen tallafawa da albashin su, kamar yadda Shugaban Majalisar Kasar ya bayyana.
A Daina Kwatanta Mu Da Na Wata Kasa – Hon Kalu
Ranar Asabar an tambayi Hon. Ben Kalu ko su na cikin shirin yin irin wannan gudummawa? Sai ya ce ai a ma daina hada su na nan Najeriya da na wasu Kasashen, saboda su nan ba su dade da kashe kudade wajen gudanar da ayyukan raya mazabun su.
Wata mujallar cikin gida da Majalisar Tarayya ke fitarwa ta bayyana cewa ana biyan dan majalisar tarayya naira milyan 2 kudin hidimar mazabu, shi kuma sanata naira milyan 5.
Kowace shekara dan majalisa na karbar albashi da akawus na naira milyan 17, shi kuma sanata naira milyan 24.
Ben Kalu ya ce rabin albashin su ba zai isa a sayi sinadarin wanke hannu ko takunkumin rufe fuska ba.