Cibiyar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta kara bayyana cewa an samu karuwar masu dauke da cutar Coronavirus a Najeriya, daga mutum 35 da ta bayyana a ranar Talata, zuwa mutum 42.
Sanarwar da Cibiyar ta buga a shafin tattara bayanan ta da kuma shafin ta Twitter a safiyar Talata din nan, NCDC ta ce an kara samun wadanda suka kamu da cutar har mutum hudu a ranar Litinin.
Cikin sanarwar, NCDC ta tantance cewa mutum 28 daga kasar waje suka shigo da cutar, domin dukkan su sun fita waje a cikin makonni biyu da suka gabata.
An kara samun mutum uku a Lagos da kuma mutum daya a Abuja.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labari a ranar Litinin cewa Najeriya ta tabbatar da karin mutum biyar masu dauke da cutar Coronavirus.
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa ce ta bayyana haka a jiya Litinin, a shafin ta na Twitter cewa an samu karin mutanen biyar ne a Abuja mutum biyu, Lagos mutum biyu said kuma da kuma Jihar Edo inda aka samu mutum daya.
An tabbatar da cewa karin mutane biyu da aka samu daga Abuja, su na daga cikin matafiyan da suka dawo daga Ingila kwanan nan, lokacin da cutar ta yi kamari a can.
Ana jin cewa dan Atiku Abubakar da ya kamu daga cutar, na daya daga cikin wadanda ake cewa sun kamu a Abuja din.
Kin Killace Kai
Babban Darakatan Cibiyar Kula da Cututtula, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana laifin karuwar yaduwar cutar daga matafiyan da suka dawo ne daga kasashen da cutar ta Coronavirus ta yi muni sosai, saboda sun ki killace kan su, kamar yadda aka yi musu gargadi.
A wata hira da aka yi da shi a Litinin din nan da safe, a gidan talbijin na Channels, Ihekweazu ya ce babbar matsalar Najeriya ita ta ce masu dawowa daga kasashen waje.
Daga nan sai ya shawarci dukkan masu aiki a kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kan su su zauna su na aiki daga gidajen su.
Sannan kuma ya ce kowa ya yi kaffa-kafda da taka-tsantsan, domin nan gaba za a kara samun rahotannin wadanda suka kamu da cutar.
Ya nuna yi bayani a kan kokarin da ake yi din zakulo sauran wadanda suka Shiva jirage daya da wasu da suka kamu.
Tuni dai gwamnatin tarayya da wasu jihohi ke ta daukar kwararan matakan hana cinkoson jama’a a wuraren ibada, shakatawa da kasuwanni domin kauce wa ci gaba da barkewar wannan annoba.
Discussion about this post