Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Barno, ta kafa dokar haramta wa jama’a kai ziyara a dukkan sansanonin masu gudun hijira na fadin jihar.
Sanarwar ta ce wannan wani muhimmin hobbasa ne da gwamnatin ke yi domin hana cutar Coronavirus yaduwa a cikin jama’a a fadin jihar Barno.
Sanarwar ta fito daga bakin Shugabar Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Barno (SEMA), Yabawa Kolo, a lokacin da ta ke gudanar da taron gaggawa da Shugabannin Kula da Sansanonin Gudun Hijira su 51 a jihar.
Ta ce wannan doka za a tabbatar da it a har tsawon makonni hudu cur.
Kolo ta ce ya zama tilas aka kafa wannan doka domin hana kai cutar Coronavirus a cikin dandazon jama’a.
“Sannan kuma rahotanni sun tabbatar da cewa wannan cuta ta bulla a kasashen da ke makautaka da Barno, irin su Chadi da Kamaru. Kuma duk da cewa an rufe kan iyakokin kasashen, wannan bai hana ci gaba da samun karuwar masu gudun hijira ba.”
Kolo ta kuma yi kakkausan gargadi ga shugabannin kula da sansanonin Gambioru Ngala, Damasak, Kalabalge, Banki, Bama da na Monguno da ke kusa da kan iyakoki cewa kada su kuskura su amshi masu gudun hijira da kusa da kan iyakokin wadancan kasashe da Najeriya.
Cikin makon da ya gabata ne Gwamna Babagana Zulum ya nada kwamitin hana yaduwar cutar Coronavirus a jihar, a karkashin Mataimakin Gwamna, Umar Kadafur.