Coronavirus: Sama da mutane 100,000 suka warke a duniya

0

Akalla sama da mutane 100,000 da suka kamu da cutar Coronavirus ne suka warke a fadin duniya, kamar yadda wata kididdiga waga rumbun tattara bayanai na worldometers.info ya nuna.

Duk da cewa cutar sai kara yaduwa ta ke yi, ta yadda har ta shiga kasashe 192 a duniya, kuma kullum ana samun yawaitar karuwar masu kamuwa, a gefe daya kuma ana samun yawan wadanda ake kulawa da magani masu warkewa ana sallamar su.

Ya zuwa ranar Litinin karfe 5:54 agogon Najeriya, an kididdige cewa mutum 101,069 ne aka tattabar da sun warke daga cutar Coronavirus a duniya.

Abin Fargaba

Sai dai kuma yayin da ake murnar samun yawaitar masu warkewa daga cutar, a gefe daya kuma iron yadda ta ke kara yaduwa a duniya da kuma yawan wadanda ta ke kashewa, ya na kara jefa jama’a a cikin firgita da zaman zullumi.

Ya zuwa ranar Litinin karfe 5:54 agogon Najeriya, an samu karin mutum 30,796 wadanda suka kamu da cutar a fadin kasashe 195 na duniya. Kuma rahotanni sun tabbatar da cewa a kasar Amurka ce aka fi samun wadanda suka kamu din kwanan nan.

Kididdigaggun bayanai sun tabbatar da mutane 7,309 sun kamu a Amurka, wasu 4,789 sun kara kamuwa a Italy, Spain kuma an kara samun mutum 4321, Jamus mutum 3,992 sai kuma Iran mutum 1,411.

Zuwa yanzu dai mutane 368,226 ne suka kamu a duniya tun daga farkon bullar cutar cikin watan Disamba, a birnin Wuhan da ke Gundumar Hubei a kasar Sin.

Yayin da har yanzu babu wani takamaimen maganin wannan cutar, ana ci gaba da shawartar jama’a su ci gaba da daukar matakan kariyar kamuwa ta hanyar kauracewa da kuma kula da tsaftar da ake ci gaba da yin bayani a fadin duniya.

Share.

game da Author