Coronavirus: Da mu bari ‘yan Chana su dawo su ci gaba da aikin titin jirgi gara mu dan hakura kadan – NRC

0

Hukumar Jiragen Kasa ta Kasa NRC, ta bayyana cewa cewa za a samu akasi kadan akan shirin da aka yi ba kammala aikin titin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan a dalilin rashin ma’aikata.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya shaida wa manema labarai cewa a yadda suka so shine a kaddamar da titin jirgin Legas zuwa Ibadan a watan Afrilu.

” Amma hakan ba zai yiwu ba saboda a ma’aikatan kamfanin da suka aikin kwangilan wato CCECC wadda kamfanin ‘yan Chana ne duk suna Can Chana ba su dawo ba.

” Ma’aikatan sun tafi hutun sabon shekara wadda a daidai za su dawo sai cutar coronavirus ya barke a kasar.

” Su kan su gwamnatin kasar ba za su bari su shigo Najeriya ba saboda wannan cuta.

Amaechi ya ce maimakon saboda muna so a kammala aiki da wuri mu daddako wa kan mu fitinan da zata addabe mu. Domin neman kiba mu samu rama.

” Domin a lokacin aka samu matsala ko wani ya dawo mana da cutar coronavirus, kun ga maganar titin jirgi ya kare kenan. Mun dinga fafutikar yadda za muyi da mutanen mu kenan ba don kawai muna son a gama aikin titin jirgin kasa.

Amaechi ya ce za a hakura kawai tukunna har sai an samu sauki matuka a duniya game da cutar in yaso sai su dawo su cigaba aiki.

Share.

game da Author