Fadar Shugaban Kasa ta yi kakkausar suka dangane da yadda jaridun kasar nan suka maida hankali wajen fifita labaran Coronavirus.
Kakakin Yada Labarai na fadar, Garba Shehu ya shiga shafin sa ba twitter ya yi wannan sukar a ranar Lahadi da dare, inda ya bayyana cewa:
“Kakaf manyan jaridun kasar nan a yau kowace na dauke da labarin cutar Coronavirus a shafin ta na farko a matsayin babban labari. Ko sai yaushe za su fara sanar wa jama’a irin yadda zazzabin maleriya ke kashe ‘yan Najeriya 822 a kullum?”
Sai dai kuma wannan bayani na Garba Shehu ya janyo masa hantara da tsangwama daga ‘yan Najeriya da dama. Su na ganin bai kamata Shehu ya taso da wannan tashin-tashina a yanzu ba.
Da dama na ganin cewa ba gaskiya ba ne a ce a kullum zazzabin maleriya na kashe mutum 822 a Najeriya.
Wasu da dama kuma na ganin idan har mutum 822 din na mutuwa sakamako da musabbabin zazzabin maleriya, to gwamnatin Buhari ce ta kasa a bangaren ladiya kenan.
Hat yau dai mutum daya daga kasar Italy aka samu da cutar a nan Najeriya, bayan ya shigo da ita a wata ziyarar aiki da ya kai masana’antar siminti ta Lafarge da ke Ewokore, cikin jihar Ogun.
Am ce ya je ne domin duba wasu na’urorin aiki da wani kamfanin kasar Sweden ya samar wa kamfanin.
Dan Italy din dai ya sauka Dulin Jirgi na Murtala Mohammed da ke Lagos. Ministan Lafiya ya ce an auna Baturen a filin jirgi da na’urar gwaji, amma ba ta nuna ya na dauke da kwayar cutar ta Coronavirus ba, saboda ba ta kai ga bin jikin sa har zuwa matakin yadda za a iya tabbayar ana dauke da ita ba.