Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da sanarwa cewa shugaban ya yi kira ga ‘yan Najeriya cewa kowa ya kwantar da hankalin sa, dangane da bullar cutar #Coronavirus.
PREMIUM TIMES ta buga labarin bullar cutar a karon farko a Lagos, bayan da wani Baturen Italy ya shigo cikin kasar nan dauke da cutar.
Tun bayan killace shi da aka yi a Lagos, Najeriya da sauran jihohi da dama suka fara daukar kwararan matakan yin kaffa-kaffa, ta hanyar wayar da kan jama’a dangane da matakan kariya ko kauce wa kamuwa da cutar.
An kuma bada rahoton killace wasu ‘yan Chana su uku a jihar Filato, tare da wasu ‘yan Najeriya su 39 da ke wa ‘yan Chana din aikin hakar ma’adinai.
A jihar Cross River gwamnatin jihar ta dukufa wajen yin amfani a mai shela da kuma cikin coci-coci ta na fadakar da jama’a cikin yare daban-daban.
Cikin sanarwar da Garba Shehu, Kakakin Yada Labarai na Buhari ya fitar, Buhari ya ce ‘yan Najeriya su daina firgita, domin yawan firgitar zai iya yi wa Najeriya illa, maimakon yin tasiri.
Buhari ya nuna jimamin yadda aka samu wani ya shigo da cutar, duk kuwa da irin karfafan matakan da aka dauka domin guje wa hakan.
Ya kuma gode wa hukumomin lafiya na kasa, na Jihar Lagos da na Jihar Ogun dangane da kokarin gaggawa da suka dauka wajen gano mai dauke da cutar.
Daga nan ya ce a daina firgita, maimakon haka, kowa ya rika kiyayawa da matakan kariya da na kaucewa daga kamuwa, wadanda ake ta sanarwar su a kafafen yada labarai badan-daban.