Bijirewa umarnin Buhari da batutuwa 9 kan Katsalandan din Abba Kyari a Harkokin Tsaro

0

Takardun bayanan korafe-korafe da gargadin da Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a kan Tsaro, Babagana Monguno ya yi dangane da katsalandan din da Abba Kyari ke yi wa harkokin tsaro, sun kara nuna yadda Shugaban Ma’aikatan ke kara zama karfen-kafa, tarnaki da dabaibayin samar da tsaro a kasar nan.

1. Shure umarnin da shugaban kasa ya kakaba na umarni

Monguno duk a cikin kwafe-kwafen takardun, ya zargi Kyari da ture umarnin Shugaba Buhari gefe daya, sannan ya kawo na sa umarni ya ce su ne za a yi a matsayin Buhari ne ya ce a yi. Alhali Buhari bai san danyar wainar da ake toyawa wa.

Masu sharhi a soshiyal midiya dai sun ce Kyari ya tabka babban laifin cin amanar kasa. Domin shi na shugaban kasa ba ne.

2. Abubuwan da Premium Times cikin kwanaki biyu ta fallasa, sun kara tabbatar da dalilin da ya sa tsawon lokaci aka rika samun sabani tsakanin Manyan Shugabannin Fanmonin Tsaro, har kowa ba ya tuntubar kowa, wanda hakan ya janyo matsalar tsaro a kasar nan.

Monguno ya shaida musu, ciki har da Tukur Buratai cewa daukar umarni daga Kyari da suke yi, babban laifi ne a dokar Najeriya.

3. Hakan ya nuna Mashawarcin Buhari Kan Tsaro, da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, su na da mummunan sabani sosai a tsakanin su. Sabanin ya rika faruwa a gefe daya kuma kasar nan na ci gaba da fama da matsalar tsaro.

4. Kakagidan da Kyari ya yi a fadar Buhari ta kara jefawa da fallasa badakalar da ke faruwa a kewaye da shi.

Kyari ya yi katsalandan a rikicin MTN, cikin 2015. Haka Sahara Reporters ta taba bugawa a baya.

5. Kyari ya hana Aisha Buhari samun sakewa da kusanci da mijin ta, Shugaba Buhari. Sai da ta kai ta fito har sai biyu ta yi korafi a fili cewa wasu ‘yan kakuduba sun kewaye Buhari, su na yin yadda suka ga dama.

6. Wannan rikici ya kara tabbatar da labarin da PREMIUM TIMES ta taba bugawa a kan yadda Kyari ya kwace shirin gina RUGA daga hannun Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo. An buga labarin cikin Nuwamba, 2019.

7. Sai Bango Ya Tsage

Kyari ya samu karin daurin gindi daga wajen Buhari. Saboda bayan an sake rantsar da Buhari a karo na biyu, cikin 2019, ya bayar da umarni cewa duk ministoci da sauran manya, su nufi Kyari kafin su garzayo wurin sa a kan duk wasu batutuwa da suka shafi aikin gwamnati.

Buhari bai ware ya ce banda mataimakin shugaban kasa ko manyan shugabannin tsaro ba.

8. An fallasa wata kwatagwangwamar kwangilar kayan aikin ‘yan sanda da aka kulla aka sa wa hannu cikin 2016 da wani gogarman dillali, mazaunin Dubai.

9. Kyari ya sha kiran Shugabannin Tsaron Kasa ana taron sirri, ba da sanin Monguno ba. Kuma ya sha kiran Jakadun Kasashen Waje ya na ganawa da su, ba tare da sanin Monguno ba ko ministan harkokin waje.

Share.

game da Author