RIKICI A FADAR BUHARI: Monguno ya fallo takobin gwabzawa da Abba Kyari

0

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa Babagana Monguna, ya zargi Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da yi wa harkokin tsaron kasa katsalandan da saka baki a abubuwan da ba shi da iko akai.

A dalilin haka Mongonu ya aika wa manyan hafsoshin Najeriya dake shugabantan rundunonin tsaro na sojoji da wasikar gargadi cewa kada su kuskura su rika karbar umarni daga Abba Kyari daga yanzu.

A wasikar da PREMIUM TIMES ta gano, Monguno ya ce a lokutta da dama Kyari ne ya ke yin gaban kansa yake ba manyan hafsoshin rundunar sojoji umarni ba tare da Shugaban Kasa Buhari ya sani ba, kuma hakan ya na kawo wa harkokin tsaro cikas matuka.

” Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba ya cikin jerin masu iya zartar da wata doka a kasar nan sannan bai yi rantsuwa don kare kasa Najeriya ba saboda haka babu dalilin da zai sa ya rika cusa baki a harkokin kasa ba.” Inji Janar Monguno.

” A dalilin haka bai kamata sannan sabawa doka ce ya rika ganawa da ta musamman da manyan hafsoshin Najeriya da shugabannin tsaron kasa ba, jakadun kasashen waje ba tare da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ministocin da ya kamata su na tare a zaman ba. Yin haka saba wa dokar kasa ce.

” Ire-iren wadannan zumudi, da cusa kansa a binda ba huruminsa bane da nuna isa da ba da umarni ba tare da Buhari ya sani ba da Kyari ya ke yi, suna kawo mana cikas a ayyukan samar da tsaro a kasa Najeriya da kuma koma baya da ake samu wajen tabbatar da samun nasara a ayyukan da shugaba Buhari ya sa a gaba.

Wannan wasika na Monguna ya zo ne a daidai matsalar tsaro ya dawo danye a kasar nan sanan ‘yan Najeriya na kuka akai matuka.

Idan dai ba a manta ba matsalar tsaro ya na neman ya gagagri jami’an tsaron kasar nan a ‘yan kwanakin nan.

A makon da ya gabata, an kashe wasu matafiya sama da 30 a garin Auno dake jihar Barno, sannan ko bayana shugaba Bubari ya ziyarci jihar, awowi kadan bayan ficewar sa daga garin mahara suka afkawa mazauna.

A jihar Katsina inda nan ne mahaifar shugaban Kasar, suma fama da hare-haren yan ta’adda babu kakkautawa, ko a karshen makon da ya gabata sai da mahara suka far wa kauyuka biyu dake karkashin karamar hukumar Malumfashi, inda suka babbake gidajen mutane, Rumbuna na dabbobi.

A kullum manyan hafsoshin Najeriya musamman na sojojin kasa, Tukur Buratai ya na ikirarin cewa an gama da Boko Haram amma abin dai, kai dai har yanzu jiya-iyau.

Share.

game da Author