CORONAVIRUS: Likitoci 1,716 suka kamu, wasu 6 sun mutu a Chana

0

Hukumar Kula da Lafiya ta kasar China, ta bada bayanin cewa ya zuwa ranar 11 Ga Fabrairu, Jami’an Kiwon Lafiya 1,716 suka kamu da cutar ‘Coronavirus a fadin kasar.

Hukumar ta kara da cewa akalla an samu masu cuta a fadin kasar kusan 68,000.

Baya ga jami’an kula da lafiyar da suka kamu, akwai wasu jami’an shida da cutar ta kashe tun bayan bullar cutar a cikin watan Disamba, 2019, a garin Wuhan da ke Gundumar Hubei.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi, ta ce an samu mutuwar mutum 1,665 a fadin kasar.

Sai dai kuma ta ce an samu nasarar warkar da mutum 8,096, wadanda tuni aka sallame su daga asibiti, suka koma gidajen su.

Amma kuma ta ce akwai wasu mutum 8,969, wadanda ake zargin sun kamu, amma ana kan gwaji tukunna.

Hukumar ta ce, “akwai kuma mutum har 169,039, wadanda jami’an kiwo lafiya ke sa-ido a kan su, kasancewa sun cudanya da masu cutar ta Coronavirus.

Har zuwa wannan rahoto dai mutum shida ne suka mutu a wajen kasar China sanadiyyar kamuwa da cutar.

An kuma bada rahoton kamuwar mutane sama da 500 a cikin kasashe sama da 30.

Cikin kasashen Faransa, Hong Kong, Philippines da Japan, an bada rahoton mutuwar mutum hudu.

Akalla Hukumar Lafiya ta China ta tura jami’an kula da lafiya har 25,633 a Gundumar Hubei, inda a can ne cutar ta fara bulla a birnin Wuhan.

Share.

game da Author