Masu neman a tsige Oshiomhole sun sake mamaye hedikwatar APC

0

Wasu masu zanga-zangar neman a cire Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole sun sake yin dandazo a Sakateriyar Jam’iyyar APC ta Kasa, a Abuja.

Masu zanga-zangar, wadanda suka kira kan su da suna matasan da suka damu da halin ha’ula’in da Oshiomhole ya jefa jam’iyyar ta su, sun ce dalilin sake fitowar su neman cire shugaban na APC shi ne saboda sakacin da ya nuna wajen hada rikicin da ya yi sanadiyya tun farko a ka samu barakar da a yanzu ta janyo APC ta rasa kujerar gwamnan jihar Bayelsa.

An dai kwace kujerar gwamnan Bayelsa daga APC aka bai wa PDP, inda Kotun Koli ta tsige David Lyon ana saura kwana daya a rantsar da shi, ta bai wa dan takarar PDP, Douye Diri.

Wannan ne karo na biyu a cikin watanni uku da masu zanga-zanga suka fito neman a cire shugaban na APC.

Wadanda suka yi zanga-zanga dai ba su sha da dadi ba, domin sun hadu da wasu matasa ’yan buyagi, wadanda suka rika jifar su da duwatsu.

Sun soki salon shugabancin Oshiomhole, wanda suka ce ya janyo musu asarar jihohin Zamfara, Rivers da Bayelsa da Oyo a zabukan da suka gabata.

Wasu ma’aikatan hedikwatar APC sun shaida wa Premium Times cewa jami’an tsaro ba su tanka wa masu zanga-zangar ba. Sai suka gama abin su, sannan kowa ya kama gaban sa.

A yanzu haka Oshiomhole na fada da Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, wanda shi ne ya gaje shi, bayan ya kammala zangon sa biyu ya na shugabancin jihar Edo.

Gwamnoni da daman a so a tsige shi, amma dai bas u fili sun rika nunawa.

Oshiomhole ya samu takun saka da Obaseki, saboda kokarin da ya rika yi ya zama ubangidan gwamnan na jihar da ya mulka tsawon shekaru takwas.

Share.

game da Author