A wata tattaunawar musamman da kokararren Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawan, ya bayyana cewa gobara ce kadai ta fi gwamnonin Najeriya ta’adi da mummunar barna.
Ku karanta ku ji sauran zafafan kalaman da ke cikin wannan tattaunawa, ciki har da dabarar da ya ce ita sojoji za su yi domin yin nasara kan Boko Haram.
PT: Matsayin ka a kan kiraye-kirayen sauya Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya
Babachir: Ni abin da na fahimta shi ne, Najeriya kasa ce mai wahalar sha’ani. ‘Yan Najeriya na da ‘yancin nayyana korafe-korafen su, muddin suka ga ba su samun gamsasshen sakamakon da ya kamata su samu daga shugabannin su. Su kuma shugabannin ai dama daga cikin jama’a suka fito, ba daga dama suka fado ba. Saboda haka, tilas su karbi laifukan su, idan har sun yi ba daidai ba. Hairan ko sharran.
Don haka idan a daya bangare mu da damar da za mu yi korafi ga shugaban kasa a kan matsalar tsaro, to sai kuma mu dubi dajin da ya keto tun daga karamin jami’in sojan da ya taba korar ‘yan tawayen Chadi, kuma wanda ya yin yakin Biafra, ya san jiya kuma ya san yau.
Don haka duk matakin da zai dauka, sai ya yi taka-tsantsan tukunna.
PT: Kai mene ne matsayin ka, kasancewa ka dade a baya a cikin gwamnati?
Babachir: To ka ga ni dai dan yankin Arewa maso Kudu ne. shi kuwa shugaban kasa na da ikon cire Manyan Hafsoshin Tsaro, dama kuma shi ya nada su. Zai iya cewa sun biya bukatar da aka nada su don su biya. Su kuma ‘yan Najeriya ai dimokradiya mu ke yi. Su kuma su na da ‘yancin cewa sun kai mu ga nasara, ko kuma sun kasa.
PT: Za ka iya cewa wannan gwamnatin ta kasa a fannin tsaro ku kuwa?
Babachir: Zan iya yin jayayya da duk wadanda ke cewa rashin tsaro na karuwa a yanzu. An yi okacin da Boko Haram ke mamaye da yankuna masu yawan gaske a Arewa maso Gabas, ta yadda ba iya ratsawa yankunan.
A jiha ta Adamawa, akwai lokacin da kananan hukumomi bakwai ke a karkashin Boko Haram. Amma yanzu ba haka ba ne.
A baya gadan-gadan su kan kai wa garuruwa da sansanoni hari. Yanzu sai dai su yi yakin sunkuru. Wadanda ba su ganin wani abin alheri a wannan gwamnatin, masu son cusa rudu ne kawai.
PT: Batun korafe-korafen sojoji ba su samun kulawar kirki sosai.
Babachir: To ka ga dai ni tsohon soja ne. Alokacin mu ko hutu soja ya tafi, to za a lisafa kudin alawus din kowa a ba shi. Kuma za su ba mu abinci. Amma a yanzu abin duk bah aka ya ke ba.
Yakin Kato da Kato Tsohon Salo Ne – Babachir Lawal
Akwai abubuwan da suka kamata a kara ingantawa a fannin sojoji. Domin idan ka shigo da tsare-tsare masu illa, ai ba ka sani ba, watakila wata rana abin zai iya shafar ka, ko wani dan uwan ka.
Ina mai tunanin cewa daga cikin abin da ke haifar mana da matsalar tattalin arziki, har da makudan kudaden da aka narkawa a bangaren sojoji.
Saboda bam guda daya ya na lashe milyoyin kudade. Shi ma harsashe da bindigogi ba arha gare su ba.
Duk da dai ni ba masanin harkokin tsaro ba ne, to akwai bukatar inganta bangaren sojoji,
Akwai matsala fa, tilas sai sojojin mu sun daina yakin gaba-da-gaba da sojoji. Wannan tsohon salo ne. Fasahar zamani ake yaki yanzu. ‘Drones’ ake yaki yanzu da sauran na’urorin zamani. Ba yakin kato da kato ba.
Sai kuma an tashi tsaye an bankado masu daukar nauyin Boko Haram. Wa ke ba su kudi? Wa ke ba su muggan makamai da abinci?
Sai dai kuma duk da wannan, na yarda da cewa a matsayin Shugaban Kasa na Janar na soja, to na yarda cewa ya san abin da ya ke yi.
Sai da dan takara nagari APC za ta ci zaben 2023 – Babachir Lawal
PT: Ya ka ke ganin APC za ta kasance a zaben 2023, ganin yadda rikici ya dabaibaye ta?
Ka ga dai mun rasa Adamawa, Zamfara, Rivers har da Oyo. Wannan kuwa duk rikin cikin gida ne ya haifar da su. Tilas sai mun tashi tsaye mun dinke barakar da ke cikin mu.
Kafin zaben 2013 ya zo. Maganar yin nasara ko rashin nasara kuwa, wannan duk ya danganta ga nagartar dan takarar da aka tsaida a wurin zabe.
Amma dai idan har ana son yin nasara, to tabbas sai an sake yi wa APC garambawul.
Batun naira bilyan 37 da za a bai wa Majalisa ta yi kwaskwarima
Ai ba a rungumo kudi a bai wa wani ko wasu. Kamata ya yi su fito da dukkan bayanai, tsare-tsare da kuma dalla-dallar yadda ko irin ayyukan da za a yi da kudaden. Amma ba ka gabatar da zunzurun uwar kudi, ka ce su ka ke so a ba ka, ba tare da yin bayani dalla-dalla kuma gamsasshe ba.