Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS), ta sanar da cewa tsadar rayuwa ta karu daga kashi 11.98 a ciikn a watan Disamba, zuwa kashi 12.13% cikin watan Janairu.
NBS wadda ta bayyana wannan rahoton na ta, ta ce ta na auna tsadar rayuwar ce da hauhawar farashin kayayyaki.
Hukumar ta ce daga Disamba zuwa Janairu, kusan kowane nau’in kayan masarufi sai da ya fuskanci karin farashi.
“Gwauron tashin da kayan masarufi suka rika yi daha watan Janariru 2019 zuwa Disamba, 2019, ya kai kashi 11.83%, amma kuma zuwa Janairu sai da ya kai 11.98%.
Kididdigar ta ci gaba da bayyana cewa tsadar rayuwa a birni ta kai gejin kashi 12.78% a watan Janairu. Amma kafin nan, a watan Janairu ba ta wuce kashi 12.62% ba.
A cikin yankunan karkara kuwa, tsadar rayuwa ta tashi daga kashi 11.41% a watan Disamba, zuwa kashi 11.54 cikin watan Janairu.
An samu karin hauhawar farashin mai, nama mai kitse, kifi, tumatir, doya biredi da suran su.
Ana ci gaba da kukan tsadar rayuwa a fadin kasar nan, har ta kai ana kiran da halin kuncin da jama’a ke ciki da sunan ‘Nes Lebul.’
Akwai masu ganin cewa rufe kan iyakoki da Buhari ya yi, yawan korar matasa masu kananan sana’o’i, kamar hayar baburan acaba da Keke Napep, ya kara haifar da korafe-korafen tsadar rayuwa.