Mutanen gari sun yi wa basaraken da ya gwaggwabji wani basarake zanga-zanga

0

Al’ummar garin Ayedie, Olaoluwa da Iwo a jihar Osun sun gudanar da zanga-zangar neman a hukunta basaraken da ya gwaggwabji wani basarake a masarautar ta su.

Sun gudanar da wannan zanga-zanga ne a kan titinan Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Zanga-zangar ta biyo bayan Oluwo na Iwo, Abdulrosheed Akanbi ya gwaggwabji basaraken Agbowa na Ogboagba, Dikhrullah Akinropo.

Sun bukaci a dakatar da shi, saboda ya ci mutumcin daraja kima da kwarjinin sarauta da al’adar Yarabawa da suka gada kaka da kakanni.

Haka su ma sarakuna sun nemi a hukunta shi, domin ya zubar da girman sa kuma girman kujerar sarautar da ya ke a kai ya tozarta wani basaraken.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Basaraken Abdulrosheed Akanbi, wanda shi ne Oluwo na Iwo a Jihar Osun, ya ajiye girman timin rawanin sa gefe, inda ya rika naushin basarake Dhikrulahi Akinropo, a kan rikicin gona.

Karin abin kunya da takaici shin ne an yi wannan rashin mutuncin zubar da girman sarauta a ofishin Mataimakin Su Feto Janar na ‘Yan Sanda na Shiryyar Osun, a birnin Osogbo.

PREMIUM TIMES ta ji cewa Sarki Akanbi ya rufe Sarki Akinropu da naushi a baki, a daidai lokacin da ake taron sasanta su a ofishin AIG, a kan wata rijimar filaye da suke yi wanda ke garin Iwo.

Majiyoyi da suka san abin da ya rika faruwa a baya, sun shaida wa wakilin mu cewa “a gaskiya tuni da dadewa Sarki Akanbi ya yi gargadin hana wasu masu rike da sarautu su daina sayar da filaye ba tare da sanin sa ba.

Sannan kuma an yi ta kokarin shirya taron zaman sasanta sarakunan guda biyu, amma abin ya ci tura, har ta kai sai da aka dangana da ofishin Shugaban ’Yan Sandan Shiyya na Osun.

A wurin taron sasantawar a ofishin AIG, akwai wasu sarakuna har guda hudu.

A na daidai tsakiyar taron ne kawai kafin a Ankara, sai Sarki Akanbi ya mike tsaye, ya rufe Sarki Akinropo da duka.

Ko kafin Shugaban ’Yan Sanda (AIG) ya farga, an yi wa Akinropo laga-laga da dukan da kyar ya kwace shi.

Daga nan da ya ke jikin say a yi tsami sosai, an garzaya da shi asabtin Asubiato da ke Osogbo, inda ake kula da shi. Kuma an ce ya na samun sauki, amma dai ya daku.

Duk da dai rundunar ‘yan sandan Osun ba su ce komai ba, wani basarake da ya ziyarce basaraken a gadon asibaibiti, ya tabbatar da an yi dukan. Sai dai ya nemi a sakaya sunan sa.

Sarki Olu na Ileogbo, Habeeb Adetoyese, wanda ya yi magana da manema labarai a madadin sauran sarakuna, ya shaida cewa Oluwo ne ya rubuta wa Gwamnantin Osun takardar korafin cewa wasu sarakuna na saida filaye.

‘Gwamnatin jihar ta nemi a je a yi sulhu, aka nemi zama a a Iwo, amma Oluwo da kan sa ya ki halarta.”

“Daga nan an kira mu ganawa da AIG a ofishin sa a ranar 14 Ga Fabrairu. Lokacin da Agbowu ya musanta zargin ya sayar da filaye, sai Oluwo ya mike tsaye a cikin fushi ya rika naushin sa. Ya ji ma saciwo a baki kafin AIG ya kwace shi.”

Shi kuwa Akanbi ya ce tabbas ya kai naushi, amma ya yi don ya kare kan sa domin ya ga Akinropo ya daga kwagirin sa, ya na kokarin ya zungurar masa idanu.

An tuntubi Kwamishinar Yada Labarai na Jihar Osun, Funke Egbemode, inda ta ce Majalisar Masarautun Jihar Osun na taron daukar matsaya domin daidaita al’amurra da kuma sanin mataki na gaba da za a dauka.

Share.

game da Author