Gwamnatin jihar Sokoto za ta ciyo bashin Naira biliya 65.7

0

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa za ta ciyo bashin Naira biliyan 65.7 domin samar da ababen more rayuwa a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Saidu Umar ya sanar da haka wa manema labarai bayan tashi taron kwamitin zartaswa na jihar.

Umar ya ce gwamnati za ta kashe wadannan kudaden ne wajen gina gidaje domin ma’aikatan jihar, kara yawan asibitoci a jihar, inganta fannin ilimi, samar da ruwan sha, inganta aiyukkan noma da inganta aiyukkan fannin shari’a a jihar.

Ya ce gwamnati ta zata ware Naira miliyan 550 domin siyo janaretoci 200 da za yi amfani da su wajen samar da ruwa mai tsafta sannan za a kashe Naira miliyan 140 wajen siyo kayan aikin samar da ruwa.

“Gwamnati za ta bude asusu da Naira biliyan 4 a babban bakin Najeriya domin ba manoman a jihar bashi don noma.

“Za kuma a kashe Naira biliyan 3 wajen siyo takin zamani domin siyar wa manoma a farashi mai sauki.

Umar ya kuma kara da cewa gwamnati za ta ware Naira biliyan 10 domin biyan ‘yan kwangilan da za su yi aiki a fannin ilimi na jihar.

“Za a kashe Naira biliyan biyar wajen kara yawan asibitoci a jihar sannan a kashe Naira biliyan 1.5 wajen gina gidajen ma’aikatan gwamnati a Gidan Salanke.

“Za kuma a kashe Naira miliyan 320 wajen siyo sabbin motoci wa ma’aikatan fannin shari’a sannan a kashe Naira biliyan 1 domin shire-shiryen aikin hajjin bana.

A karshe kwamishinan yada labarai Isah Bajini-Galadanchi yace gwamnati za ta karba kuma ta biya bashin kudaden tare da riba a cikin shekaru 3 sannan bashin ba zai shafi gwamnatin da za ta zo nan gaba ba.

Share.

game da Author