Abinci 7 dake kawar da matsanancin damuwa – Likita

0

Wasu likitoci da suka kware a duba masu fama da tabuwar hankali sun yi kira ga mutane da su guji yawan saka kansu cikin matsanancin damuwa cewa yin haka na daga cikin abubuwan dake haddasa tabuwar hankali.

Mutum kan fada cikin matsanancin damuwa ne idan bashi da halin samun biyan wani bukata ko kuma samun wani abu da aka sa a gaba.

Sai dai kuma abinda ba a sani ba shine yawan saka kai cikin damuwa baya sa a samu biyan bukata sai dai a fada cikin hadari da ya kan kai ga tabuwar hankali a lokutta da yawa.

Sai da wata likita mai suna Marissa Laliberte a kasar Amurka ta bayyana cewa akwai wasu abinci dake dauke da sinadarin da suke taimakawa wajen hana mutum fadawa cikin matsanancin damuwa.

An wallafa wannan bayanai ne a shafin ‘THE Healthy’ dake yanar gizo.

Ga abincin.

1. Ayaba

Ayaba na dauke da sinadarin ‘Vitamin B6’ wanda idan mutum ya ci jikinsa zai samu sinadarin ‘Neurotransmitter Serotonin’ wanda ke ingantawa da sa fara’a zuciyar mutum.

Marrisa ta ce karancin wannan sinadari a jikin mutum yakan sa a fada cikin matsanancin damuwa.

2. Ruwa

Marrisa ta ce shan ruwa na cikin hanyoyin gujewa fadawa cikin matsanancin damuwa.

Ta kuma ce bai kamata sai an ji kishi ba kafin a nemi ruwa. Karancin ruwa a jikin mutum na cutar da kiwon lafiya.

3. Beat

Beat wani abu ne dake kama da dankalin Hausa sai dai shi ja ne a ciki da waje.

Ana iya cin wannan abu danye ko kuma dafaffe amma masanan sa sun ce mutum zai fi samun sinadarin inganta kiwon lafiya ne idan an ci danye.

Beat na dauke da sinadarin ‘Folate’ wanda ke taimaka wa wajen hana damuwa.

4. Kifi

Kifi na dauke da sinadarin ‘Omega 3’ wanda ke kaifafa kwakwalwar mutum.

A dalilin haka likitan ta yi kira ga mutane da su rika cin kifi domin lafiyar kwakwalwarsu.

5. Alkama

Bincike ya nuna cewa alkama na cikin abincin dake sanya farin ciki domin likitoci kan shawarci matan da suka daina haihuwa da su rika cin alkama domin gujewa fadawa cikin matsanancin damuwa.

6. Bakin alawan cakulat (Dark chocolate)

Likitoci sun ce shan coco rigakafi ne waje guje wa kamuwa da cututtukan hawan jini, ciwon siga,karfafa karfin ido da sauran su.

7. Cin ‘ya’yan itatuwa

‘Ya’yan itatuwa kamar su tuffa, lemo,Plums, fiya, gwaiba da sauran su na sanya farin ciki wa mutum sannan idan ana shan shayi mara madara ma na taimakawa wajen haka.

Share.

game da Author