ZAZZABIN LASSA:Mutane 9 sun kamu da cutar, 4 sun rasu a jihar Kogi

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Kogi ta sanar cewa mutane 9 ne suka kamu sannan wasu 4 sun rasu tun da zazzabin lassa ta bullo a watan Janairu a jihar.

Shugaban masu gudanar da bincike kan cututtuka na jihar Austin Ojotule ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Lokoja ranar Lahadi.

Ojotule ya ce a ranar 8 ga watan Faburairun 2020 sun gwada jinin mutane 31 inda daga ciki suka gano cewa mutane 9 sun kamu da cutar sannan 4 daga cikin su sun rasu.

Ya ce an gano mutanen da suka kamu da cutar ne a kananan hukumomin Ibaji, Okene, Idah, Okehi, Igalamela.

Ojotule ya ce sun kuma gano mutane 177 wadanda suka yi mu’amula da wadanda suka kamu da cutar.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ya nuna cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 285 sannan 41 sun rasa rayuwar su a dalilin kamuwa da wannan cuta a kasar nan.

A dalilin haka kungiyar likitoci (NARD) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ayyana dokar tabaci akan zazzabin lassa ganin yadda cutar ke ta kara yaduwa a kasar nan.

YADDA ZA A KIYAYE DAGA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

5. Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

6. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

7. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

8. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

9. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

10. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

11. Kona Daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

12. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.

Share.

game da Author