Ba za a iya cire Shugabannin Tsaro a yanzu ba – Sakataren Gwamnati

0

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa a halin da ake yanzu ba za a iya cire Shugabannin Tsaron kasar nan ba.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana haka, duk kuwa da irin kiraye-kiraye da korafe-korafen da ake yin a a cire su, saboda tabarbarewar tsaro a kasar nan.

‘Yan Najeriya da dama sun yi ammana cewa manyan shugabannin tsaron kasar nan babu sauran wata dabarar tsaron kasar nan da ta rage musu, a kokarin ganin an kawar da Boko Haram da kuma hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane a kasar nan.

Wani neman jin ra’ayin jama’a da PREMIUM TIMES ta gudanar a shafin ta na intanet, ya nuna cewa akasarin wadanda suka kada kuri’a, kashi sama da 70 bisa 100 sun nemi a cire shugabannin tsaron.

Su ma Majalisar Dattawa ta yi wannan kuka, wanda kusan ma daga can ne aka fara neman a cire su.

‘Ba Za A Cire Su Ba Yanzu’ – Gwamnatin Tarayya

A kokarin san a kare gwamnati, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya fada a ranar Talata cewa bah aka kai tsaye ake cire mutane irin wadannan ba.

“Ba a tashi kawai haka katsahan a cire mutane irin wadannan. Akwai tsare-tsare da matakai da kuma jiran lokacin da ya kamata, ko lokacin da damar cire su din ta samu.

“An wayi gari muna cikin wani mawuyacin hali. Mu na bukatar kowa da kowa ya kawo ta sa gudummawa. Mu na bukatar sa-ido daga al’umma a cikin abin da ke faruwa cikin su da kuma kewayen su.

“To idan mu ka sake mu ka fara samar da kafar shigar sabani a wannan mawuyacin hali, wa ne ne zai amfana? Ai magauta ne za su yi amfani da sabanin kenan su kara cimma burin su na ganin sun hargitsa kasar nan.” Inji Mustapha.

Mustapha ya yi wannan jawabi ne a wurin kaddamar da littafin tarihin Sakataren Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, Samuel Salifu.

A jawabin sa, Shugaban Kungiyar CAN ta Kasa, Samson Ayokunle, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ya yi dukkan kokarin da za ta iya yi domin tabbatar da cewa ta murkushe Boko Haram da kuma sauran ayyukan bazaranar zaman lafiya da suka addabi kasar nan.

“Idan suka yi haka, sun kyauta wa al’ummar kasar nan, kuma sun kyauta wa kan su. Amma idan ba su yi ba, to tarihin su zai cika da kasawar su, ba nasarorin su ba.” Inji Ayokunle.

Share.

game da Author