Monguno ya sake caccakar Abba Kyari kan kememe da yayi a kwangilar siyo makamai

0

Mai ba shugaban Kasa Shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ya sake caccakar shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa, Abba Kyari, inda yace da gangar yake kaucewa daga umarnin Buhari yayi kan gaban sa a harkokin da bai shafe shi.

Wannan sabon korafi ta fito ne daga wata takardar sirri da PREMIUM TIMES ta samu mallaki inda ya ke nuna yadda Monguno ya rika caccakar Abba Kyara yana nuna cewa yana yi wa harkar tsaro katsalandan a kasar nan.

A wasikar Mongunu ya ce Abba Kyar bashi da ikon saka baki a harkar tsaro sannan hatta siyo wasu kayan aiki da za a yi wa ‘yan sandan Najeriya da yayi katutu a akai ba hurumin sa bane.

Babban dalilin caccakar sa da yayi kuwa shine yadda kiri-kiri, ya canja bayanan wata kwangilar siyo makamai da aka saka hannu tsakanin gwamnatin Najeriya da Kasar UAE.

Monguno ya bayyana a wasikar da ya rubuta da ya aika wa Ministan tsaro, Sufeto janar din ‘yan sanda da sauran su cewa lallai fa su sani wannan cusa hannu da Abba Kyari yake yi a harkar tsaro zai iya sa a rika wa Najeriya dariya sannan a rika ganin bata san abinda ta ke yi ba domin kuwa babu abinda ya hada shi da maganan tsaro.

Sai dai kuma ba mu iya gano ko wani kwangila bane da kuma irin dimbin makaman da ya kamata ace an siyo har an shigo da su tunda tun a shekarar 2016 ne shugaban Kasa Buhari da Yerima na kasar UAE suka saka hannu akan takardar yarjejeniyar siyo makaman.

Kokawar Monguno da Kyari

Maiba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa Babagana Monguna, ya zargi Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da yi wa harkokin tsaron kasa katsalandan da saka baki a abubuwan da ba shi da iko akai.

A dalilin haka Mongonu ya aika wa manyan hafsoshin Najeriya dake shugabantan rundunonin tsaro na sojoji da wasikar gargadi cewa kada su kuskura su rika karbar umarni daga Abba Kyari daga yanzu.

A wasikar da PREMIUM TIMES ta gano, Monguno ya ce a lokutta da dama Kyari ne ya ke yin gaban kansa yake ba manyan hafsoshin rundunar sojoji umarni ba tare da Shugaban Kasa Buhari ya sani ba, kuma hakan ya na kawo wa harkokin tsaro cikas matuka.

” Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba ya cikin jerin masu iya zartar da wata doka a kasar nan sannan bai yi rantsuwa don kare kasa Najeriya ba saboda haka babu dalilin da zai sa ya rika cusa baki a harkokin kasa ba.” Inji Janar Monguno.

” A dalilin haka bai kamata sannan sabawa doka ce ya rika ganawa da ta musamman da manyan hafsoshin Najeriya da shugabannin tsaron kasa ba, jakadun kasashen waje ba tare da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ministocin da ya kamata su na tare a zaman ba. Yin haka saba wa dokar kasa ce.

” Ire-iren wadannan zumudi, da cusa kansa a binda ba huruminsa bane da nuna isa da ba da umarni ba tare da Buhari ya sani ba da Kyari ya ke yi, suna kawo mana cikas a ayyukan samar da tsaro a kasa Najeriya da kuma koma baya da ake samu wajen tabbatar da samun nasara a ayyukan da shugaba Buhari ya sa a gaba.

RIKICI A FADAR BUHARI: Monguno ya fallo takobin gwabzawa da Abba Kyari

Wannan wasika na Monguna ya zo ne a daidai matsalar tsaro ya dawo danye a kasar nan sanan ‘yan Najeriya na kuka akai matuka.

Idan dai ba a manta ba matsalar tsaro ya na neman ya gagagri jami’an tsaron kasar nan a ‘yan kwanakin nan.

A makon da ya gabata, an kashe wasu matafiya sama da 30 a garin Auno dake jihar Barno, sannan ko bayana shugaba Bubari ya ziyarci jihar, awowi kadan bayan ficewar sa daga garin mahara suka afkawa mazauna.

A jihar Katsina inda nan ne mahaifar shugaban Kasar, suma fama da hare-haren yan ta’adda babu kakkautawa, ko a karshen makon da ya gabata sai da mahara suka far wa kauyuka biyu dake karkashin karamar hukumar Malumfashi, inda suka babbake gidajen mutane, Rumbuna na dabbobi.

A kullum manyan hafsoshin Najeriya musamman na sojojin kasa, Tukur Buratai ya na ikirarin cewa an gama da Boko Haram amma abin dai, kai dai har yanzu jiya-iyau.

KARANTA: EXCLUSIVE: NSA Monguno attacks Abba Kyari over police equipment contract

Share.

game da Author