Kwamitin Majalisar Dattawa mai sa-ido kan yadda hukumomin Gamnatin Tarayya ke kashe kudade, ya harzuka da bijirewar da Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Hameed Ali ke yi mata.
Ta nuna rashin jin dadin yadda Ali ke kin halardtar duk wata gayyata da aka yi masa domin ya yi mata baynin yadda aka kashe wasu kudade.
Takun-sakar baya-bayan nan dai ta faru na a ranar Talata, bayan da Shugaban Kwastan ya ki halarta ko amsa gayyatar da kwamitin ya yi masa, domin yin bayani dangane da wani zargi da Babban Mai Binciken Kudi na Kasa ya yi wa Hukumar Kwastan da Hukumar Tattara Harajin Cikin Gida ta Kasa (FIRS).
Yarfe su da karya Dokar Tsarin Fansho ta 2014, inda hukumomin biyu ba su tura kashi biyar albashin ma’aitaka a Asusun Fansho na Kasa.
A kan haka ne aka nemi su je su yi bayanin dalilin rashin tara kudaden, ko kuma a ji yadda aka yi da kudaden.
A ranar da ya kamata su halarta, sai Akanta Janar ya je Majalisar Dattawa ya yi bayani a madadin hukumomin da ake zargi din su biyu.
Yayin da Ofishin Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS) ya tura wakili a lokacin zuwa majalisar, shi kuma Shugaban Hukumar Kwastan bai je ba, bai tura wakili ba, kuma bai aika da wani uziri ba.
Da ya ke kare hukumar kwastan a lokacin, Ahmed Idris ya ce rashin wadatar kudade isassu ya sa Hukumar Kwastan ba ta tara kashi 5 bisa 100 na albashin ma’aikatan ta a Asusun Fanshon Ma’aikata.
Ya bada hakurin cewa da zaran an samu isassun kudade, to kwastan za su rika zuba kudaden ba da wani bata lokaci ba.
Rashin ganin wakilcin kwastam ya sa an sake gayyatar Hameed Ali Shugaban Hukumar da ya halarta a ranar Talata, amma bai je ba.
Shugaban Kwamtinin Majalisar Dattawa Mai Lura da Kashe Kudaden Gwamnati, Sanata Mathew Urhoghi, ya ce dabi’a da halayyar da Shugaban Kwastan ke yi ba dattijantaka ba ce, kuma ba girman sa ba ne. Sannan ya ce idan aka sake gayyatar sa ya ki halarta, to majalisar dattawa za ta yi amfani da rahoton da Mai Bin Diddigin Kudaden Gwamnatin Tarayya ya bayyana Hukumar Kwastan na aikawata cewa gaskiya ne.
“Ko ya zo ya kare hukumar sa, ko kuma mu amince da zargin da Akanta Janar na Tarayya ya yi akan abin da Hukumar Kwastan ke aikatawa cewa gaskiya ne.”
Inji Sanata Mathew.
Ya ce kuma alhakin zargin gaba daya zai koma kan Hameed Ali.