KURUNKUS: Tambuwal ya yi nasara a kotun Koli

0

Kotun Koli a Abuja ta bayyana gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal na jam’iyyar PDP a matsayin sahihin zababben gwamnan jihar Sokoto.

Duka alkalai bakwai da suka yanke wannan hukunci sun ce korafin APC ba shi da madafa.

Kotun ta wancakalar da korafin da ta shigar a gaban ta sannan ta tabbatar wa Tambuwal da kujerar sa.

Uwani Abba-aji ce ta karanta hukuncin kotun.

Idan ba a manta ba jam’iyyar APC ta kai kara ta na kalubalantar zaben Aminu Tambuwal a zaben 2019.

APC ta ce an yi mata murdiyya ne da hakan yasa ba ta kai ga yin nasara ba.

Tambuwal na Jam’iyyar PDP, ya kada Ahmed Aliyu na APC da kiri’u 300 da ‘yan kalilan ne.

Tun bayan bayyana sakamakon zaben a 2019, APC tace bata amince da sakamakon zaben ba.

Hakan yasa aka yi ta kai ruwa rana da yakai ga sai da aka kaiga garzayowa kotun koli.

Yanzu dai aukin gama ya gama, Tambuwal ne yayi nasara a kotun.

Share.

game da Author