Kotun Koli a Abuja ta yi watsi da karar da Abba Yusuf ya shigar yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnan jihar Kano.
Idan ba a manta ba, kotun daukaka kara da kotun sauraren kararrakin zabe duk sun ba da hukuncin cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne yayi nasara a zaben gwamna da aka yi a Jihar Kano a 2019.
Abba Yusuf na PDP ya garzaya kotun koli inda ya nemi kotun ta soke wannan hukunci ta mika masa kujerar gwamnan jihar Kano cewa shine yayi nasara ba Ganduje ba.
Bayan sauraren lauyoyin duka bangarorin wato, bangaren gwamna Ganduje na APC da na Abba Yusuf, na PDP kotun ta amince da hukuncin kotun daukaka kara.
A hukuncin kotun da daya daga cikin Alkalai bakwai da suka yanke hukuncin ya karanta, Sylvester Ngwuta ya bayyana cewa Abba Yusuf na PDP da jam’iyyar sa ba su iya gamsar da kotun cewa wai kotun daukaka kara ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke a baya ba.
Ya ce Abba da jam’iyyar sa basu iya tabbatar wa kotun koli cewa lallai PDP din ne ta lashe zaben gwamnan Kano ba, Zaben 2019 sannan kuma cewa wai an kacaccala takardun da aka shigar da alkaluma zabe na ainihi wanda shine ke kunshe da asalin sakamakon zabe a wasu wuraren.
A dalilin haka ita ma kotun koli ta amince da hukuncin kotun daukaka kara da ma hukuncin farko da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke cewa Abdullahi Ganduje ne ya lashe zaben Kano a 2019.
Discussion about this post