RIKICI A JIGAWA: Gumurzun makiyaya da manoma ya bar baya da kura

0

Mako daya kenan bayan barkewar rikicin da ta kai an kasfa fada tsakanin makiyaya da manoma a kauyen Fulata, cikin Karamar Hukumar Taura, amma har yau kowane bangare na dora laifin rikicin a kan daya bangaren.

Su dai Fulani na cewa manoma daga Fulata sun je sun kone musu gdidaje sun kuma lalata musu dukiyoyi tare da satar musu shanu da dama.
Amma su kuma manoman cewa suka yi makiyaya ne suka kai musu farmaki dauke da makamai a ranar Juma’a da ta wuce.

Kauyen Fulata sun yi iyaka da Karamar Hukumar Ringim. Fulanin da aka kone wa matsugunai na can su na zaman gudun-hijira cikin garuruwan Hadejia, Gumel da Kirikasamma tare da dangin su.

Sarkin Fulanin Taura, Sabo Ali, ya shaida wa manema labarai cewa an ji wa Fulani da dama rauni, ta kai da dama.

Ali ya ce, “har yanzu ba mu san ko mutum nawa aka kashe mana ba, ko kuma yawan wadanda aka jikkata. Saboda wasu da yawa ba mu san halin da su ke ciki ba tukunna.

“A yanzu haka akwai daruruwan masu gudun hijra a cikin gida na, musamman mata da kananan yara, wadanda suka tsere tun karfe 2 na dare.

Amma dai na ja hankalin Fulani na ce su guje wa tayar fa fitinar daukar fansa.

“Na sanar da Hakimin Taura, na sanr da ’yan sanda, na kuma sanar da Shugaban Karamar Hukuma dangane da abin da ke faruwa.

“Hukuma ta roke ni na yayyafa wa fitinar ruwan sanyi, ta hanyar gargadin Fulani kada su je su dauki fansa. To kuma duk mun bi wannn shawara da kiraye-kiraye.”

‘Karya Fulani Ke Yi’

Sai dai kuma dagacin Fulata, Muhammad Sule, y ace makiyayan ne suka yi musu barna. Har suka ci gonar wani Hamza.

“Fulanin da ke zaune a kewayen mu ne suka gayyato wasu bakin Fulani, suka shigo suka yi wa manoman mu barna

“An ma kama wasu shanun su wadanda aka damka su Fadar Hakimin Taura. Wannan ya kara tabbatar da cewa sun je sun yi barnar kenan.

”Daga nan kuma sai wadannan Fulani suka yi gangami, dubban su suka taso wa manoman mu domin su mamaye mu, amma jama’r mu ta fi karfin su, aka kore su.” Inji Sule.

Ya ce dama an dade ana samun samun takun-saka a tsakanin su.

“Mun sha kai kara, amma DPO da kan sa ya ce ba zai iya tunkarar Fulanin ba, saboda fitina da tashin hankalin da za su iya haifarwa daga baya. Sakamakon wannan rikici sun ji wa wasu Hausawa hudu mummunan rauni.

“A zaman yanzu haka mutane hudun da aka ji wa ciwo duk suna asibiti, amma ana kula da su, kuma sun a samun sauki.”

‘Ban san inda iyayen mu, mata ta da shanu na suke ba’

Yakubu Hussaini da Hassan Sabo sun bayyana wa PREMIUM TIMES irin raunin da aka ji musu. Sabo ya ce har yau bai san inda iyayen sa sue ba, kuma sun tsufa, gas hi kuma an shanun sa 9 sun bace.

“Na tsinci ’ya ta mai shekaru biyar a wani kauye ta na yawo tsirara. Gas hi kuma har yau ban san inda mata ta take ba.
“Ina gida tare da iyaye na masu shekaru da yawa, lokacin da manoma suka kawo mana hari. Wasu na cewa a kashe ni, wasu kuma na cewa su kyale ni. A haka dai na yi sa’a na tsere.”

A karshe dai Yakubu Hussaini ya ce ya hadu da wasu mahara, inda suka sare shi da adda, kuma suka dauke shi cikin jini suka kai shi wurin Hakimi.

A zuwa lokacin hada wannan labari dai ba a kama kowa ba.

Share.

game da Author