KEBBI A 2019: Hisbah ta cafke wasu mazaje biyu dake tarayya da Juna, mata shida da aka yi wa auren dole

0

Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta bayyana cewa a shekarar 2019 kungiyar ta tsinci jarirai 11 kuma ta ceto ‘yan mata da matan aure 20 da aka yi garkuwa da su.

Shugaban Hukumar, Abubakar Muhammad ya sanar da haka a hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a Birnin Kebbi.

Ya ce a cikin wannan shekarar kungiyar ta yi nasaran ceto yara kananan 63 da aka yi garkuwa da su sannan tuni an dankasu ga iyayen su.

Hukumar ta kuma sassanta rigingimu har guda 210 musamman a tsakanin ma’aurata, abokai, iyaye da ‘ya’ayn su a jihar.

Baya ga haka Muhammad ya ce hukumar ta damke mata 19 da suka yi ciki ba tare da aure ba, an hako jaririn da aka birne da ransa, an kama wasu mazaje biyu dake tarayya da juna, mata shida da aka yi wa auren dole sannan da yan damfara.

Ya ce kungiyar ta kama wasu matasa mazaje 12 dake lalata da mata a dakunan Otel sannan da karuwai mata 25.

An kuma kama matasa da mata 12 da suke ta’ammali da miyagun kwayoyi, mata 19 da suka zubar da ciki da mata uku da suka yi aure da ciki.

Muhammad ya yi kira ga iyaye da su kula da irin tarbiyyar da suke ba ‘ya’yan su da kuma saka ido da irin abokan da ‘ya’yan hulda da.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta farfado da ofisoshin hukumar Hisbah a sauran kananan hukumomin dake jihar cewa yin haka zai taimaka wajen rage miyagun ayyuka a fadin jihar.

Share.

game da Author