Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa yaduwar cutar kwalara ko kuma amai da zawo ya ragu zuwa kashi 60 bisa 100 a duniya.
Rahoton ya kuma nuna cewa an fi samun ragowar yaduwar cutar a kasashen duniyan da cutar ya yi wa katutu kamar su kasashen Haiti, Somalia, Jamhuriyan Kongo, Najeriya, Zambia,Kudancin Sudan,Jamhuriyan Tanzania, Somalia da Bangladesh.
Cutar kwalara ko kuma cutar amai da zawo cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cin abinci, shan ruwa ko kuma zama a muhallin da bashi da tsafta.
Manya da yara na kamuwa da wannan cuta kuma cutar na iya yin ajalin mutu cikin lokaci kalilan idan ba a gaggauta daukar mataki ba.
Bincike ya nuna cewa duk shekara mutane miliyan daya zuwa hudu na kamuwa da cutar sannan mutane 143,000 na rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar a duniya.
Binciken ya kara nuna cewa a shekarar 2018 mutane 499,447 ne suka kamu da wannan cuta inda daga ciki 2,990 ne suka mutu a kasashe 34 a duniya.
Duk da haka WHO ta ce an samu matukar raguwar yaduwar cutar a shekaran 2019 a duniya.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus yace hakan na da nasaba ne da kokarin da kasashen da cutar ya fi bullowa suka yi ne.
Ghebreyesus ya ce wannan kokari kuwa ya hada da yi wa mutane allurar rigakafi da bin hanyoyin kawar da cutar da kungiyar ta tsara.
“ A shekarar 2018 an raba maganin cutar har miliyan 18 wa kasashen duniya 11 sannan tun bayan sarafa maganin rigakafin cutar da aka yi a shekaran 2003 an raba sama da miliyan 60 na maganin rigakafin wa kasashen dake fama da cutar.
“WHO na kara jadadda cewa samar wa mutane ruwa mai tsafta da wayar musu da kai game da cutar ne babban abinda za a fi amida hankali domin dakile yaduwar cutar.