Gwamna Zulum ya hana sojoji yi wa mazauna garuruwa biyu kwasar-karan-mahaukaciya

0

Kwana daya rak bayan Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya zargi sojoji da ’yan sanda na karbar naira 1000 da kowane matafiyin da ba shi da katin shaidar dan kasa, a yau kuma ya taka wa sojoji Najeriya burki daga kwashe dubban mutanen garuruwan Jakana da Mainok a yau Talata.

A ranar Talata ne Zulum ya sake garzayawa Jakana da Mainok domin ya hana sojoji kwashe mazauna garuruwan ba tare da sanar wa Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jiha, hukumomin NEMA, SEMA da sauran jami’an tsaron da suka kamata a sanar da su ba, kafin a kwashe al’ummar.

Wakilin PREMIUM TIMES da ya je garuruwan Mainok da Jakana a yau, ya iske sojoji sun kai jerin gwanon motocin da suka fara ajiye domin kwashe mutane zuwa sansanonin masu gudun hijira a Maiduguri.

Dama kuma wakilin na mu ya bi tawagar gwamna Zulum jiya Litinin zuwa garin na Jakana, wanda Boko Haram suka kai wa hari cikin makon da ya gabata.

Jakana na kilomita 45 daga hanyar shiga Maiduguri daga Kano da Damaturu, Mainok kuwa kilomita kusan 65.

Kuma wannan hanya ce kadai mashigar birnin Maiduguri, yayin da sauran titinan duk ba su shiguwa shekaru da dama da suka wuce, saboda hare-haren da Boko Haram ke kaiwa.

A Jakana ne sojoji suka yi artabu, barin wuta da gumurzu da Boko Haram a makon jiya, a lokacin da Boko Haram din suka kai hari makon da ya wuce da dare.

Ba a san dalilin sojojin na yunkurin kwashe mutanen garuruwan zuwa sansanonin masu gudun hijira a Maiduguri ba a wannan lokaci.

Amma dai cikin 2019 sun taba kwashe mazauna Jakana, a lokacin da sojoji suka ce za su yi wani farmakin fatattakar Boko Haram da suka ce ke zaune a yankunan.

Sannan kuma sojoji sun yi zargin cewa Boko Haram na yin shigar-burtu sun a sajewa da mutanen garin, amma kuma mutanen garin ba su tona asirin su.

Yayin da wakilin mu ya isa Jakana da Mainok a yau Talata, ya bayyana cewa ya ga daukacin dandazon mazauna garuruwan tsaitsaye a gefen titi kowane dauke da kayan da zai iya dauka, su na jiran a kwashe su zuwa Maiduguri a kai su cikin sansanonin masu gudun hijira.

A kan hanya zuwa Mainok, Zulum ya ci karo da tawagar Kwamandan Operation Lafiya Dole, wanda ya tsaida gwamnan, suka kebe, kuma aka hana manema labarai matsawa kusa da su.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa Zulum ya shaida wa Kwamanda Olusegun Adeniyi cewa bai yarda a kwashe al’ummar ba, ba tare da sanar da gwamnatin tarayya, ta jiha, NEMA, SEMA da jami’an SSS, ‘yan sanda da C-JTF ba, kamar yadda ya ke a ka’ida.

Zulum yace sojoji sun yi gaggawar kokarin kwashe mautanen ba tare da sanar da gwamnati da hukumar agajin gaggawa ta kasa da ta jiha, wato NEMA da SEMA domin su yi shirin karbar dubban mutanen garuruwan biyu ba.

Gwamna Zulum nan take ya kira babban hafsan hafsoshin soja, Janar Tukur Buratai halin da ake ciki.

A lokacin da Zulum ya isa Jakana, ya yi wa al’ummar garin jawabin cewa gwamnatin jihar Barno ta na goyon bayan kokarin da sojoji ke yi domin samar da tsaro a yankin, kuma ba za ta gajiya wajen bayar da goyon bayan ba.

Amma dai duk da haka inji Zulum, kamata ya yi su sanar da gwamnati kwafin su kwashe mutanen, gudun kada su haddasa cinkoson masu gudun hijira a cikin Maiduguri.

Daga nan sai Zulum ya ja kunnen mazauna garin cewa su rika fallasa duk wani dan Boko Haram da ya shigo cikin su ya yi bad-da-bami ko basaja a cikin su.

Wakilin mu ya ji lokacin da mazauna garin ke wa Zulum korafin cewa tun karfe 5 na asubahi a cikin sanyi sojoji suka fito da su daga gidajen su har bayan 11 na safe su na tsaye gefen titi sun a jiran a kwashe su zuwa Maiduguri.

Zulum dai ya umarci kowa ya koma gidan sa, sannan ya yi bayanin cewa abu mafi muhimmaci shi ne kare lafiyar al’ummar ba wai kwashe su a maida su masu gudun hijira ba, idan aka yi la’akari da yawan su.

Share.

game da Author