BARCELONA: Ba cire Valverde, Wanda ya maye gurbin sa

0

A ranar Talata ne tsohon kociyan Barcelona, Ernesto Valverde da aka sallama jiya Litinin ya yi bankwana da kulob din a cikin fara’a da annashuwa. Ko ba komai dai, ya jefar da kwallon mangwaro, ya huta da kuda.

Mamakin da duniyar kwallo ke yi kuma shi ne yadda Barcelona ta kori Valverde, maimakon ta dauko kwararren kociya, wanda duniya ta sani, kuma ya shahara, sai ta dauko Quique Setien, tsohon kociyan da Real Betis ta kora a kakar wasan La Liga da 2018/2019, bayan da Betis din ta kare kakar a matsayin ta 10.

Duk ba wannan ne abin mamakin ba, Stien dai bai taba cin kofi ko na auna ruwan madarar-sukudaye ba, duk kuwa da cewa ya yi tsawon shekara da shekaru ya na koyarwa a kungiyoyi daban-daban.

Barcelona ta shiga rudu ko rududu cikin makon da ya gabata, inda shugaban ta Josep Maria Bartomeu ya shiga neman sabon kociya, alhali kuma ba a kori ko sallami Valverde ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sun tuntubi tsohon dan wasan ta, Xabi Harnendez da Ronald Koeman, amma duk sun noke, saboda gudun samun takun-saka da shugabannin kungiyar a karkashin shugabancin Martomeu.

Duk da haka sai da Valverde ya yi tirenin na ‘yan wasan Barcelona a jiya Litinin, duk kuwa da cewa daga rannan ya san da wahalar gaske ya sake horas da kungiyar har abada.

A karshe dai da Xabi da Koeman suka nuna rashin bukata, sai aka rubuta sunayen Quique Sutien, Gabriel Milito da Mauricio Pochettino domin a darje, a zabi daya daga cikin su.

An yi mamakin yadda Barcelona ta yi tunanin daukar Pochittino, tsohon kociyan Tottenham, mutumin da ya ce shi a duniya da ya yi kociyan Barcelona, har gara ya dauki fartanya, ya koma gona ya yi noma.

Setien, wanda shi aka dauka a matsayin sabon kociya, bai taba lashe kofi ko da na gasar wasan lido ba. Kulob din da ya horas a shekarar da ta gabata, na 10 ya zo a gasar La Liga.

QUIQUE SITIEN: Ina Kiwon Shanu Barcelona Ta Dauke Ni Kociyan Ta

A jawabin da ya yi yau Talata wurin karbar ragamar kulob din daga hannun Valverde, sabon kociya Sitien ya ce, “A jiya war-haka ina gona ta wurin kiwon shanu a kauyen mu. Yau kuma ga ni a yau kuma ni ne kociyan ‘yan wasan da suka fi kowane shahara da kwarewa a duniya.

“Ai ana yi min tayi, ko lokacin minti biyar ban bata ba, sai na ce na amince, na karba.”

Shi kan sa Sitien ya yi matukar mamakin yadda Barcelona ta dauke shi koyar da wasa a kungiyar ta, kungiyar da a yanzu haka ita ce ta farko a La Liga.

Valverde Ba Dan-goyo Ba Ne

Ba cire Valverde ne ya fi ba masu kallo da masu sharhin kwallon kafa mamaki ba, maye gurbin sa da Sitien shi ya fi bada mamaki ga kowa, har ma ga ‘yan wasan kungiyar.

An yi tunanin za a cire Valvade tun shekarar 2019, bayan da Liverpool ta yi wa kubob din cin-kaca a gasar Champions League, cin-wulakancin da Barcelona ba ta taba kwasar buhun-kunya kamar sa ba, a tarihin kafuwar kungiyar.

Harkallar Cinikin ’Yan Wasa

Shugabannin Barcelona sun samu kan su cikin kwatagwangwamar cinikin ’yan wasa, yayin da suka bi ta barauniyar hanya suka sayi Neymar lokacin shugabancin Sandro Rossell, wanda Bartomeu ya gada.

Daga baya kotu ta daure Sandro shekaru biyu, bayan samun sa da aka yi da laifin harkalla.

Shi ma Bartomeu sai da aka zarge shi da damfara, amma dai ya yi ta shige-da-fice ya na kokarin kare kan sa.

Da Asara Gara Gidadanci

Sandro da Bartomeu sun hada kai sun sayar da Neymar ga PSG fam milyan 222, wadanda suka kwasa suka sayi Phillppe Coutinho da Ousmane Dembele da kudin. Sannan kuma suka sayi Douglas da Prince Boateng, wadanda ba su tsinana wa kulob din komai ba.

Tun bayan tafiyar Johan Cruyff da Pep Guardiola, Barcelona ta saki kyakkyawan salon ta da duniya ta san ta da shi – wato salon a taka muku leda, a kunyata ku, kuma a jefa kwallo a ragar ku.

Sai kulob din ya fara take-taken neman ‘sa’a-dai-nasara-dai’ a karkashin Tata Martino, Luis Enrique da kuma Valverde wanda aka sallama jiya Litinin.

An san sabon kociya da sha’awar irin salon takun wasan da Cruyff da Guardiola suka koyar. Ya zama wajibi idan ya na so ya tsira da mutuncin sa, to ya ci gaba ko kuma ya dawo da irin na su salon, ko kuma kafar sa ta kai shi inda ya fito, tun lokacin tafiyar sa bai kai ga yi ba.

Babbar akidar da Guardiola ya rike, kuma ta kai shi ga nasara, ita ce La Masia, wato kyankyashewa, raino da kuma yaye kananan yara daga karamin kulob din Barcelona zuwa babban kubob. Sai kuma dauko kananan yara daga wani wuri a raine su a kulob din.

Hana rantsuwa Luis Enrique ya raini Sergi Roberto, shi kuma Valverde ya raini Ansu Fati. Amma kananan yara hatsabibai irin su Carle Alena da Dani Olmo, sun kauce tun da aka bada aron su, ba su sake komawa Barcelona ba.

Tun bayan tafiyar Guardiola sai wannan salo ya shiririce, iyayen yara suka rika korafin cewa ba su sanin halin da tasirin yaran su ke da shi. Wasu yaran kuma maimakon a shigar da su cikin babban kulob, sai aka rika tura su wasu kungiyoyi ana bada aro ko lamunin su.

Yawa-yawan yaran idan sun tafi, kowa sai ya kama gaban sa, ba ya sake komawa ta kan Barcelona.

Saurin Fushi Kan Abu Kadan

An dauki tsohon mai tsaron gidan Barcelona, Victor Valdes domin koyar da karamin kubob din Barcelona wasa, amma kwanan sa 80 kacal aka kore shi, saboda ya yin tankiya da Daraktan Koyar Da Kananan Yara Kwallo, wato Patrick Kluivert, wanda shi ma tsohon dan wasan Barcelona ne.

Ire-iren wadannan misalan su na da yawa. Kusan dalili kenan Carles Puyol, Jordi Cruyff da kuma a yanzu Xavi Harnendez suka yin baya-baya da aiki a Barcelona, a takaice har sai shugabannin da ke rike da kulob din sun kammalla wa’adin su, an zabi wasu tukunna.

Gwanitta da kwarewar Lionel Messi ta taimaka wa Barcelona tun bayan barin Guardiola daga kulob din.

Amma idan ka tsame Messi shi kadai daga Barcelona, to za ka ga sauran ’yan wasan kusan duk tubalin-toka ne.

Hausawa dai na cewa ‘komai darajar sa ke saida shi’. Shin ko Barcelona za ta yi dan-karen tsada a karkashin sabon kociya Sitien?
Mu dai sharhi ne na mu. Sannan kuma ’yan kallo ne mu, ba ‘yan wasa ba.

Share.

game da Author