RUNDUNAR AMOTEKUN: Dattawan Yarbawa sun maida wa Gwamnatin Tarayya raddi

0

Kungiyar Dattawan Kare Muradin Yankin Yarbawa da Kungiyar Shugabannin Yankin Middle Belt, sun maida wa Gwamnatin Tarayya raddi mai zafi dangane da haramta‘Yan Sandan Tsaron Jihohin Yarbawa, wato Amotekun.

A ranar Talata ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa dakarun wadanda aka kafa cikin karshen makon da ya gabata, ba bisa dokar kasar nan aka kafa su ba, don haka haramtattu ne.

Wadannan shugabanni na yankuna biyu dai sun bayyana cewa Jawabin da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi na bayyana dalilan haramta Kungiyar cin zarafi ne kuma wani kokari ne na dankwafewa ko danne ‘yancin wani bangaren kasar nan wanda ya ke da shi a karkashin zamantakewar shiyyoyin kasar nan kasa daya dunkulalliya.

Malami ya ce kafa Amotekun bai hallata ba, domin dokar Najeriya ta bayyana karara cewa: “Babu wata Gwamnatin Jiha ita kadai, ko kuma tare da wasu jihohi da za su ware su kafa wata kungiya ko hukuma domin kare al’ummar Najeriya ko wani yanki na jihohin su.”

Wasu ‘yan Najeriya da dama sun rika sukar gwamnatin tarayya ganin yadda ba ta haramta hukumomin Hisbah na Jihar Kano da Zamfara ba, amma kuma ta haramta Amotekun.

Da dama na ganin cewa kotu ce kadai za ta iya haramta kungiyoyin idan akwai kwararan dalilai da hujjojin da kotun za ta dogara da su.

Tsayar Dattawan Yarbawa Da Na ‘Middle Belt’

Dattawan ‘Middle Belt’ da na Kudancin Najeriya sun ce bayanin Ministan Shari’a Malami ya kara jefa su cikin shakkun cewa lallai gwamnatin tarayya ta kyale yankunan su makiyaya da sauran mabarnata na kai musu hare-hare, ba tare da an magance musu ba.

Kakakin Kungiya, Yinka Odumakin ne ya fitar da sanarwa a jiya Talata, inda shi da sauran wakilan Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu kuma ‘Arewa ta Tsakiya’ ko kuma a ce ‘Middle Belt’ suka sa wa hannu.

“ Mun fada wa Gwamnonin Kudu maso Yamma cewa su yi watsi da bayanin da Ministan Shari’a Malami ya yi, su garzaya kotu su kalubalance shi. Domin shi ba kotu ba ne da zai fito gatse-gatse ya haramta Amotekun. Saboda ba zamanin mulkin soja mu ke ciki ba, ballantana a yi masa karfa-karfa.

“ Mu na jajircewa da cewa abin da gwamnonin jihar Kudu Maso yamma suka shi, shi ne daidai domin ta hana ne kawai za sun iya karewa da tsare lafiya da dukiyoyinn al’ummar su, kamar yadda doka ta tanadar.

Daga nan kuma sun kalubalanci Malami da ya fito fili ya bayyana wa duniya dalilin halascin CJTF da aka kafa a wasu jihohin kasar nan, domin tsaron lafiya da rayukan al’umma a Arewa.

Ku Tafi Kotu Ku Nemi ‘Yancin Ku –Lauya Mike Ozekhome

Babban lauyan nan masanin dokokin Najeriya, Mike Ozekhome, ya yi kira ga gwamnonin Kudu maso Arewacin Kasar nan su garzaya kotu domin su kwato ’yancin su na kafa Ametokun.

Ya yi wannan bayani ne jin kadan bayan da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta haramta ‘yan sandan tsaron jihon Lagos, Ondo, Ogun, Oyo, Oshun da Ekiti, wadanda aka kafa a karshen makon da ya gabata.

Lauyan ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu wata hardaddiyar matsala tsakanin Ametokun da dokar Najeriya.

Daga nan sai ya ce Ministan Shari’a ya tabka kuskure da ya haramta kungiyar.

Ya ce ya zama wajibi a yanzu a kyale jihohi su rika kare yankunan su, gwargwadon irin kalubalen matsalar tsaron da ke addabar kowace jiha.

Share.

game da Author