Kotun koli ta bayyana Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Imo duk da shine ya zo na hudu a zaben gwamnan da aka yi a watan Maris.
Da take karanta hukuncin kotun, maishari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana cewa bayan sauraren lauyoyi da bayanan da aka gabatar an gano cewa hukumar zabe ta soke kuri’u a mazabu 388 wanda APC ce ta lashe zaben wadannan mazabu.
” Bayan mun duba kuma mun tabbatar da haka sai muka sake kirga kuri’un da hukumar zabe ta soke a wadannan mazabu.
” Sakamakon da muka samu ya nuna mana cewa wadannan tabbas APC ce ta yi nasara aka soki da karfin tsiya. Bayan haka sai muka hada wadannan kuri’u duka da wadanda aka kirga daga baya sai muka samu cewa kuri’un da APC ta samu yafi na sauran Jam’iyyun.
Wannan shine dalilin da ya sa dukan mu alkalai muka amince cewa ba a bayyana ainihin sakamakon zaben ba kamar yadda ya auku a jihar a wancan lokaci.
” Muna umartar hukumar zabe da ta karbe shaidar da ta ba Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP ta mika wa Hope Uzodinma na jam’iyyar APC sabuwar shaidar yin nasara a zaben watan Maris 2019.
kotun ta dage bada hukuncin zaben Sokoto da Kano sai ranar Litini mai zuwa.
Discussion about this post