Ban yarda cewa Dakarun Amotekun barazana ne ga Najeriya ba -Tinubu

0

Jagoran Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnonin Kudu maso Yamma su zauna tare da Ministan Shari’a Abubakar Malami domin su samu maslaha wajen sabanin da gwamnonin suka samu da Tarayya a kan kafa Dakarun Amotekun.

A cikin jawabin da ya fitar a ranar Laraba, Tinubu ya ce bai yarda da surutun da wasu ke yi cewa wai Amotekun za ta zama barazana ga tsaron kasar nan ba.

Sai dai kuma ya ce zama a kan tuburin tattaunawa tsakanin gwamnonin Kudu Maso Yamma da Minista Malami zai sa kowane bangare ya fahimci batutuwan dai bai gane ba, ko kuma inda ya daure masa kai.

Tinubu wanda ya yi magana a karon farko kan kafa Dakarun Amotekun, ya ce zafafan kalamai da wasu ke fesawa su ne abin tsoro ba kafa Amotekun ba.

Ya ce wadanda ke surutun cewa kafa Dakarun Amotekun barazana ce ga tsaron kasar nan, to su na nuna wani shisshigi ne kawai a kan abin da ba hurumin su ba ne.

“Haka nan su ma masu kallon cewa gwamnatin tarayya na kokarin dankwafe Kudu maso Yamma, to gigitattu ne.

“Da masu cewa Amotekun barazana ce ga tsaron kasa da masu cewa Gwamnatin Tarayya na kokarin dankwafar fa Kudu maso Yamma, duk sun makance, sun dimauce sun afka ramin son rai a gigice.

Ya ce bin damuwa ne matuka cewa mutanen da ba su ma gama sanin hakikanin abin da abu ya kunsa ba, sai su fito su na hayagagar da ba ta dace ana furtawa a kasar nan ba.

“ Wadanda ke sukar Amotekun na yi ne kawai saboda ‘yan siyasar su na sukar shirin kawai. Wasu kuma na suka ne saboda sun ga babu ta yadda za a yi su ci amfani ko moriyar shirin.

Daga nan ya kara da cewa shi bai ga wani aibi daga shiri da tunanin da gwamnonin Kudu maso Yamma suka yi na kafa Amotekun ba.

Sannan kuma Tinubu ya kara da cewa bai ga wani mugun nufi, nifaka ko wata makarkashiyar dankwafe wani yanki daga bayanin da Ministan Shari’a ya yi a kan matsayar sa da Amotekun ba.

Sai dai kuma ya nuna rashin jin dadin yadda wasu suka rika watsa kalaman lallai su na so su ji ya fito da gaggawa ya bayyana ra’ayin sa a kan Dakarun Amotekun ba.

Ya ce wadanda suka rika kiraye-kirayen ya fito ya bayyana ra’ayin sa da wuri, sun yi ne don kawai su ji idan jagoran na APC ya yi wata kasassaba, su kuma su yi amfani da kamalan na sa domin biyan wata bukata ta su ta siyasa.

Tunibu ya yi magana a kan kalubalen matsalar tsaron da kasar nan ta samu kan ta a ciki, kama daga yankin Kudu Maso Yamma, na Arewa da ma kasar baki daya.

Share.

game da Author