Yadda sojoji suka aika ’yan Boko Haram 48 lahira a daren Kirsimeti

0

A gumurzun da aka yi a bayan garin Biu da ke kudancin Barno, daren Laraba, sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan Boko Haram 48.

Wani jami’in ‘yan-sakai na CJTF ne da mambobin su suka taya sojoji yakin ne ya shaida wa PREMIUM TIMES haka.

Sai dai kuma har yanzu bangaren sojoji ba su bayyana adadin Boko Haram din da suka kashe din ba.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Boko Haram suka sake tattaruwa bayan garin Biu da nufin sake afkawa cikin garin, sa’o’i 24 bayan sojoji sun fatattake su a ranar Litinin.

A ranar Litinin din sai da Boko Haram suka tarwatsa kauyuka Biu tare da kashe mutane biyu da ji wa 13 raunuka, kafin daga nan suka darkaki Biu.

To daga nan ne sojoji suka yi kukan-kura suka tunkare su, suka fatattake su.

Kai Hari na Biyu a Biu

Misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata kuma sai mazauna garin Biu suka samu labari mai tayar da hankali cewa an ga wasu mutane da ake zargin Boko Haram ne sun tattaru kusa da kauyen Kimba, wani dan kauye da kusa kwarai da Biu.

Wata majiyar cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa daga nan fa aka yi sauri aka haka gangamin dakarun sojoji daga sansanoni daban-daban, domin tunkarar Boko Haram din gadan-gadan.

Majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa sojojin Biu da na Damboa sun hadu suka tunkari Boko Haram aka rika musayar kazamar wuta, tun daga cikin dare, har wayewar safitar Laraba, ranar Kirsimeti.

“Ba a nan abin ya tsaya ba, domin su ma dakarun sa-kai na CJTF sun kai dauki, inda yaki ya yi tsanani, har aka yi nasarar kashe Boko Haram 48, wasu kuma suka tsere da harbin bindigu a jikin su.”

Mohammed Liberia, kamar yadda ake kiran sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an ci gaba da kafsa yaki har bayan karfe 4 asubahi, inda suka bi suka tattara gawarwakin Boko Haram 48 da suka kashe.

Daga nan ya ce sun kama wasu Boko Haram uku da ran su.

Share.

game da Author