Wani dan Najeriya da ya yi gudun hijira zuwa Amurka cikin 2017, yam utu a kurkukun jami’an kwastan na Amurka da ke cikin Jihar Maryland.
Jami’an Kwastan a Maryland sun bayyana cewa sunan dan Najeriya din Akinyemi, kuma ya na da shekaru 56.
Ya mutu ranar Asabar, bayan jami’ai sun same shi a sume, cikin kurkukun da ya ke a Shiyyar Worcester County, a kan tsauni Dusar Kankar, wato Snow Hill.
Rahoto dai ya nuna cewa har zuwa yanzu ba a san takamaimen dalilin rasuwar sa ba.
Amma kuma kuma jami’ai sun hakkace cewa kashe kansa ya yi cikin kwana daya da ka kai shi kurkukun aka tsare.
Jami’an yankin sun tabbatar da cewa marigayi Akinyemi ya shiga Amurka daidai yadda doka ta gindaya, sai kuma bayan zaman sa ne sai ya ki bin umarnin da ke shimfide cikin ka’idojin da Amurka ta tanadar wa bako.
An kuma tabbatar da cewa ana cajin sa da laifin yin lalata da karamar yarinya, inda aka same shi da laifi a kotun Birni ta Baltimore.
Cikin watan Mayu ne PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa akwai ‘yan Najeriya har 29,723 wadanda suka makale cikin kasar Amurka suka ki dawowa Najeriya, kuma duk wa’adin zama kasar da aka bai wa kowanen su ya wuce.
Dimbin ‘yan Najeriya na zaune Amurka, wasu na karatu, wasu ayyuka, wasu kuma sana’o’i daban-daban a ko’ina cikin jihohin Amurka.