Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun damke magidancin da ya kashe matarsa saboda tsananin duka da yayi mata.
Mutiu Sonola surfafi matar sa Zainab Shotayo da dukan tsiya ne har sai da ta mutu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa mahaifin Zainab ne ya kawo karar wannan magidanci caji ofis.
Mahaifin Zainab ya shaida mana cewa, yana gida a kwance aka kira shi cewa ga Mutiu nan yana lakadawa yar sa Zainab dukan tsiya a gida. Nan da nan sai ya tashi maza-maza ya nufi gidan su Zainab. Ko da ya isa sai ya iske yarsa kwanshe sharaf.
” Daga nan sai ya jijjibeta sai asibiti. isar su ke da wuya sai likta ya saida masa cewa ai rai yayi halin sa. Zainab dai ta rasu.”
Shi ko Mutiu na jin haka sai ya arce ya bar gida. Allah cikin ikon sa jami’an Yan sanda suka fantsama neman sa har Allah ya basu ikon cafke shi.
Yanzu dai yana tsare ana ci gaba da gudanar da bincike akan sa.
Discussion about this post