Jami’an tsaro na SSS sun yi wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja shigar-kutse, sun sake kama Omoyele Sowore, kwana daya bayan sun sake shi.
Al’amarin ya faru yau Juma’a da safe, inda SSS suka yi kokarin karya kofar kotun domin kutsawa ciki.
Da yake kama su Sowore na da masaniyar haka, sai lauyoyin sa da abokan arziki suka ki fita da shi waje, suka yi zaman su a kotun.
Sowore ya je kotu ne tare da lauyoyin sa, kwana daya bayan sakin sa da Mai Shari’a Ijeoma ta bada umarni a yi cikin awa 24.
Ya je kotun ne domin ci gaba da sauraren ba’asin yadda SSS suka danne masa hakkin sa, suka tsare shi har watanni hudu, wato kwanaki 124.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=flnn9TkEBv8&w=560&h=315]
Mai Shari’a Ijeoma da ke shari’ar karar da aka shigar da Sowore kan zargin yi wa kasa zagon kasa da kuma aibata Shugaba Muhammadu Buhari, ya jajirce dewa tilas sai SSS sun bi umarnin da kotu ta bayar sun saki Sowore, domin ya cika sharuddan beli.
An saki Sowore jiya Alhamis da dare, bayan da Mai Shari’a ta yi raga-raga da hukumar SSS, ta ce su na maida kan su kamar wata kotu, saboda ba su bin umarnin kotu.
Har yanzu dai ba a san takamaimen dalilin ya sa SSS suka sake yinkurin kama shi ba a cikin kotun, a safiyar yau Juma’a.
An nuno wani bidiyo yadda ake kokawa tsakanin jami’an SSS da kuma lauyoyi da abokan arzikin Sowore.
Yayin da SSS ke kokarin yin cacukui da Sowore, su kuma lauyoyin sa da abokan arziki su na kokawar hana Sowore kubucewa daga hannun su.
Akwai cikakkun bayanai tafe an jima.