Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Alhamdulillah, muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki, Mai kowa, Mai komai, mamallakin komai da komai, da yasa al’ummar duniya, masu hankali, masu ilimi, masu adalci, masu hangen nesa, masu tsoron Allah, suka shaida cewa lallai wannan bawan Allah, wato Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II shi ake zalunta, kuma shi ake yiwa hassada da ganin kyashi akan matsayin da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bashi.
Madalla, domin ko wannan kadai babbar nasara ce a gare shi. Don haka sai mu kara gode wa Allah akan wannan.
Allah ya ja zamanin Sarki, hakika abun da ka riga ka sani ne, babu abun da zan nuna maka, ka kara godiya ga Allah akan baiwar hakuri da juriya da jajircewa da yayi maka. Ka sani, Allah ya dade da ran Sarki, hakuri ya kan daga darajar mutum ta yadda baya tsammani. Don haka idan kaci gaba da yin hakuri, kaci gaba da dogara ga Allah kamar yadda ka saba yi din nan, hakika wallahi daga karshe kai ne mai cin nasara daga dukkan makiyan nan naka da suke neman ganin bayan ka. Sannan ka sani, domin babu wani karatu da zan nuna maka, shi wannan hakuri yana daga cikin manyan dabi’u na Musulunci, yazo a cikin Alkur’ani a wurare da dama cewa, mai hakuri shine da cin riba a duk inda zai fuskanta, kuma a ko wane hali ya samu kan sa a ciki. Allah Ta’ala yana cewa:
“Lallai Allah yana tare da masu hakuri.”
Kaga anan kuwa, duk wanda yake tare da Allah, ai wallahi yafi karfin kowane shedani, mutum ne shi ko Aljan.
Kamar yadda ka sani ne, hatta fiyayyen halitta ma, wato Annabi Muhammadu (SAW), bai tsira ba daga irin wadannan abubuwa ba. Tarihin sa da sirar a fili suke ga duk mai son sanin hakan. Amma daga karshe, da yayi hakuri, kuma ya jajirce da dukkan irin jarabawar da ya hadu da ita, sai Allah ya dora nasara a hannun sa, kuma ya turmusa hancin makiyansa, ya tozarta su.
Makiyan sa sun kore shi daga mahaifarsa wato garin Makkah, ya koma garin Madinah, suka kafa daula, har aka yi fatahu Makkah aka yada addini, addini ya shiga duk inda ake so, ya shiga ko wane lungu da sako na duniya. Su ma Khalifofin sa shiryayyu, da sahabban sa, ba’a bar su a baya ba, haka suka yi har Allah yasa aka karbi daular rumawa, farisawa da sauran su, wanda duk mun sani, sai da suka yi hakuri, suka nuna jajircewa da juriya, da dogaro ga Allah, sannan suka samu wannan nasara da daukaka.
Shi yasa ma Annabi (SAW) ya fada a cikin Hadisi ingantacce cewa, wadanda suka fi shan wahala da haduwa da jarabawa da kalubale iri-iri, sune Annabawa da Manzannin Allah; sannan masu bin su sune mutanen kirki, salihai, da masu riko da addinin Allah. Gwargwadon gaskiyar ka da rikon ka da addinin Allah, gwargwadon jarabawar da zaka hadu da ita. Wannan abu sananne ne a wurin ka, da wurin dukkanin Malaman Allah da Annabi.
Akwai Annabin Allah daga cikin Annabawan sa da yayi wa jama’ar sa wa’azi, ya fada masu gaskiya, sanadiyyar haka suka jefe shi, suka dake shi, suka yi masa jina-jina, yana cikin jinin sa, ya daga hanun sa sama, yace ya Allah ka yafe masu don basu san ni Manzon Allah ba ne.
Wallahi na sani, daga cikin masu adawa da kai, ya Mai Martaba, akwai wadanda suke jahilai ne, basu san komai ba, basu san irin matsayi da darajar da Allah yayi maka ba. Kawai an dora su ne akan wannan tafarki na kiyayya da kai. Kamar yadda na sani, kuma a cikin su akwai wadanda sun san ka, kuma sun san ko kai waye, amma cuta irin ta hassada ta hana su mika wuya ga abunda Allah yayi.
Allah ya taimaki Sarki, abu ne sananne, kuma tabbatacce a tarihi, wanda ba wanda ya isa ya shafe shi, cewa, magabatanka ma sun hadu da irin wannan jarabawa, sun hadu da kalubale iri-iri, kala-kala, daban-daban, daga hannun magabtan su. Kuma duk duniya ta shaida cewa, lallai sun yi hakuri, sun jajirce, daga karshe sai Allah ya dora nasara a hannun su, ba don komai ba, sai don gaskiyar su da ikhlasin su. Shi yasa har gobe, al’ummah tana yi masu addu’a, su kuwa makiyan nasu, sai Allah wadarai da la’anta da tsinuwa kawai suke haduwa da su daga wurin mutane.
Kai ma, wallahi, mun shaida, ya Mai Martaba, duk wadannan masu adawa da kai, sai ka ga bayansu, kamar yadda magabatanka suka ga bayan makiyan su. Ba don kamai ba sai don gaskiyar ka, amanar ka, da kyakkyawar manufarka akan ci gaban ko wane mahaluki.
Ya Mai Martaba Sarki, mu dai kam, Allah ya sani, babu abunda har kullun za mu fada maka, illa mu ci gaba da maimaita irin abun da Sayyidah Khadijah (RA) ta fada wa mai gidan ta, wato fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW), a lokacin da ya hadu da mala’ika, ya matse shi. Annabi ya dawo gida a firgice, cike da tsoro da razani. Wannan mata gwarzuwa, wadda duniya ta shaida nagartar ta, me ta fada wa Annabi (SAW) a wannan lokaci, don ta kwantar masa da hankali? Ga abin da ta fada kamar haka:
“Wallahi Allah ba zai taba kunyatar da kai ba, ba zai taba tozarta ka ba, ba zai taba wulakantaka ba har abada! Domin kuwa kana sada zumunci, kana daukar nauyin mutane, kuma kana taimaka wa mara shi, kuma kana mutunta bako, kuma kana taimakawa gaskiya da masu gaskiyar.” [Sahihul Bukhari]
Wannan, ya tabbatar muna da cewa, duk mai irin wadannan halaye, Allah ba zai taba kunyata shi ba. To mu kuwa mun shaida, kuma za mu yi shaida, har a gaban Allah, akan cewa, Mai Martaba Sarki, wadannan halayen ka ne, kuma dabi’un ka ne. Da wannan muke dada tabbatar maka da cewa, In Shaa Allahu, Allah ba zai taba bari a wulakanta ka ba! Duk wani sharri da makirci, In Shaa Allahu zaka tsallake shi, zai zama tarihi da karfin ikon Allah!
Hakika hakuri yana daga matsayin mutum a wurin Mahaliccin sa. Ina rokon Allah, don tsarkin Sunayen sa, ya kara wa Mai Martaba Sarki hakuri, juriya da jajircewa; kuma ya bashi ikon cinye duk wannan jarabawa, amin.
Sannan muna kira ga dukkanin al’ummah, da su sani, wannan al’amari na Mai Martaba Sarki, ba magana ce ta Darika da Izala ba. Mai Martaba Sarki dai shugaba ne na kowa da kowa. Shi shugaban ‘yan dariku ne, kuma shi shugaban ‘yan Izala ne, kamar yadda yake shugaba ga hatta salafiyyun, kai da ma wadanda basu danganta kan su ga kowace irin tafiya. Don haka mu ji tsoron Allah, domin naji wai wasu gungun ‘yan Izala, suna kokarin yin martani ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi akan wasu maganganu na nasiha da yayi zuwa ga Gwamnan Kano Ganduje, wadanda suke duk wani mai adalci yasan cewa wadannan nasihohi ne na gaskiya, wadanda babu wani son zuciya a cikin su.
Don haka, su sani, wannan abu da suke son yi, wani kokari ne na sake raba kan al’ummar Annabi Muhammadu (SAW), da kuma kunna wutar rikici da fitina a cikin al’ummah. Kuma duk alhakin wannan, wallahi zai sake komawa ne kan wadancan ‘yan siyasa, masu son tarwatsa kan al’ummah da rarraba su, domin cimma wani buri nasu na duniya ko na siyasa. Kuma wadannan mutane Allah ba zai bar su ba. Tun anan duniya sai sun ga sakamakon aikin su, kafin muje lahira, uwa uba!
Sheikh Dahiru Bauchi Malamin addini ne, kuma jagora, sannan kuma shi yana kokarin kare gaskiya ne a duk inda ta ke, kamar yadda mun san cewa wannan ita ce dabi’ar duk wani malamin Allah, don ita ce hanyar Annabawa da Manzannin Allah; wato kare gaskiya a duk inda ta ke. Su sauran malaman da suka zabi su kama bakin su, suyi gum, suyi shiru akan wannan jarabawa ta Mai Martaba Sarki, saboda tsoron ‘yan siyasa, ko don kwadayin wani dan abin duniya, ya rage nasu, kuma su sani cewa, za su tsaya a gaban Allah, mahaliccin su, gobe kiyama domin su amsa tambayoyi. Shi dai Sheikh Dahiru Bauchi ya sauke nauyin da Allah ya dora masa, yayi wa Gwamna Ganduje nasiha. Yaji ko kar yaji wannan kuma dabam, kuma idan yaki ji, kan sa zai cutar da yardar Allah.
Dukkanin mu mun san Hadisin Manzon Allah (SAW) da yayi umurni akan taimakon wanda aka zalunta:
“UNSUR AKHA KA ZALIMAN AU MAZLUMAN…”
Duk wani malamin Allah da Annabi, kai da dukkanin wani mutumin kirki, Musulmi ne shi ko Kirista, wallahi ba za su kame bakin su suyi shiru ba, alhali suna kallon wasu gungun azzaluman ‘yan siyasa, suna neman yin dirar mikiya akan wani mutum daya daga cikin al’ummah, sai fa idan wannan al’ummah ta zama munafukar al’ummah. Wanda yin haka kuwa, na tabbata, zai jawo wa wannan al’ummar fushin Allah. Allah ya kiyaye, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.
Discussion about this post