KATSINA: Yadda masu garkuwa suka kutsa sakandare suka arce da mutane

0

Wasu mahara dauke da manyan bindigogi sun kutsa rukunin gidajen kwanan malaman Sakandaren Kimiyya ta Dutsinma a jihar Katsina, suka arce da mutum uku.

Rundunar ‘yan sandan Katsina ta tabbatar da arcewar da aka yi da mutanen uku.

Wadanda aka tsere da su aka yin garkuwar dai duk ‘yan gida daya ne. An gudu da matar maigidan, kanwar ta da kuma jinjiri daya.

Matar da aka tsere da ita din dai matar Shamsuddeen Yusuf ce, wani malami a Babbar Kwalejin Ilmi Mai Zurfi ta Isa Kaita, a Dutsinma.

Kakakin Yan sandan Katsina, Gambo Isa, ya ce maharan sun shiga cikin rukunin gidajen a ranar Litinin suka sace mutanen uku. Amma ya ce jami’an tsaro har da DPO na Dutsinma duk su na bakin kokarin ganin sun ceto su.

Ya kara da cewa an hakkake masu garkuwar sun fito ne daga Dajin Rugu da ke makwautaka da Kananan Hukumomin Dutsinma, Safana, Batsari da Kurfi.

Har zuwa Laraba dai wadanda suka gudu da su dai ba su kira kowa ba, ballanatana a ji abin da suke so a biya su diyya kafin su sake su.
“Wannan ne karo na hudu da aka shiga Dutsinma aka yi garkuwa da mutane a cikin wata daya.

Na farko sun karbi kudi daga wani mai suna Danbello.

“Sannan kuma sun kai hari a gidan main a Mamu Oil wajen karfe 9:30 na dare suka bindige maigadin gidan mai din. Suka gudu da wani mai suna NasiruIbrahim Dandanku, wani jami’in kwastan. Ba su sake shi ba sai da suka amshi naira milyan hudu.”

Garin Dutsinma da garuruwan kewayen sa sun dade su na fama da masu garkuwa da mutane.

PREMIUM TIMES ta ji daga majiya mai tushe cewa farkon 2019 sai da aka shafe kwanaki 61 ana shiga garin ana garkuwa da mutane.

Idan ba a manta ba, a cikin Dutsinma ne aka shiga da rana tsaka aka yi garkuwa da mahaifiyar mai gidan mai na Shema Oil.

Sannan Kananan Hukumomin Safana, Batsari da Kurfi da Danmusa da suka sha fama da masu garkuwa da mutane, duk su na makwautaka ne da Dutsinma, kuma duk a cikin Dutsinma aka kirkire su, bayan kirkiro jihar Katsina.

Yanzu haka kauyukan cikin Karamar Hukumar Kurfi na fama da masu garkuwa da mutane, yadda kauyuka da dama jama’a na barci da ido daya.

Idan ba a manta ba, cikin garin Wurma da ke Karamar Hukumar Kurfi, kusa da Dutsinma ne aka yi garkuwa da mutane sama da 40 a cikin wannan shekara.

Wurma na kusa da garin Birchi, inda mahara a shekarun baya suka yi takakka har gida suka kashe dagacin garin, wanda mahaifi ne ga fitaccen ma’aikatacin Sashen Hausa na BBC ne, Aminu Abdulkadir.

Cikin wannan wata na Disamba ne mahara suka shiga kauyen Yarliya’u da ke kusa da Kurfi, suka saci mutane uku.

Kafin nan kuma watannin baya sun dira Yarliya’u sun saci Kansilan Mazabar Barkiya, suka saci Kansila da matar sa.

Sabon Layi da ke kusa da Kurfi akan hanyar Dutsinma can ma mazauna garin sun sha fama da masu garkuwa da mutane.

Kwakkwarar majiya kuma ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa jiya Talata mahara a cikin dajin Jibiya sun kafa shinge suka tare masu sumogal din shinkafa suka yi musu fashi.

Majiyar da ta tabbatar da an yi fashin amma ba ta tabbatar da adadin ko buhunan shinkafa nawa aka kwace wa masu sumogal ba, ta ce an ce sun kwace buhunan kimanin 200.

Duk da sasansatawar da ake gani gwamnatin Katsina, a karkashin Aminu Bello Masari ta yi da masu garkuwa da mutane, kamar yadda Gwamnatin Bello Matawalle ta yi, wannan bai hana masu garkuwa da mutane ci gaba da shiga yankunan jihar Katsina su na tasa keyar jama’a sun a garkuwa da su ba.

Share.

game da Author