Kungiyar kwallon fata ta Barcelona ta buga kunnen doki da abokiyar kafsawarta, Real Madrid a filin Nou Camp dake garin Barcelona.
Real Madrid ta kusa kwance wa Barcelona zani a Kasuwa a lokutta da yawa a lokacin da ake wannan gwabzawa.
Wasan dai bata yi kamar a gidan Barcelona ake buga ta ba domin Madrid duk da ba su da Ronaldo sun rika kai wa Barcelona hari akai-akai.
Mai tsaron bayan Barcelona, Terstagen ya taka rawar gani matuka inda ya rika ture zafafan kwallaye daga kafafuwan Casemiro, Bale, da Benzima.
Messi bai nuna bajintantar sa ba a wannan wasa duk da cewa shine ya lashe kambun Ballon d’Or ta shekarar 2019.
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona sun fice daga gidajen kallon kwallo a Najeriya a fusace su kuma ‘yan Madrid suna ta Kuwwa da ife-ife na nuna murna rike Barcelona gadagau da taka mata birki da tayi a gida suka hana su sakat.
Za a sake gwabzawa a karo ta biyu a shekara mai zuwa, wato 2020.
Discussion about this post