Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Sarki Auwalu shugaban Sashen kula da Albarkatun man fetur ta kasa DPR.
Mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar Laraba.
Sarki Auwalu zai shugabanci wannan ma’aikata na tsawon shekaru 4 a karo na farko.
Sanarwan ta bayyana cewa Sarki Auwalu ya kammala digirin sa ta farko a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, Kafin ya ci gaba da karatu a Jami’ar Bayero sannan ya zarce zuwa kasashen waje domin samun kwarewa a aikin sa.