Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya bayyana cewa akwai wasu manyan kalubale da suka dabaibaye Najeriya.
Garba Shehu ya na magana ne a matsayin martanin da ya mayar wa tsohon babban hafsan soja, Alexander Ogomudia.
Tsohon hafsan sojan dai an ruwaito shi ya na cewa za a iya kawo sauyi a Najeriya ne kawai ta hanyar tashin hankali.
A na sa raddin, Shehu ya ce “Furucin Ogomudia ya nuna irin abin da ke cikin zukatan irin mutanen da har yau ba su karbi dimokradiyya a matsayin tsarin shugabanci na farar hula ba.
“Ganin yadda wanda ya yi wannan furucin tsohon babban hafsan soja ne, ya kamata a sani cewa a matsayin mu na al’ummar da ke kasa daya dunkulalliya, kasa ce da aka dora a kan dimokradiyyar da ke tafiya a turbar doka da tsarin mulki.
“Saboda haka ya zama tilas mu rika taka-tsantsan da bin tsarin dimokradiyya, idan kuwa bah aka ba, duk abin da aka yi akasin haka, to ba a kan doka ya ke ba, kuma kwansitushin ba ta amince da yin haka din ba.
Fadar ta tunatar cewa ga shi wannan dimokradiyya da aka kafa ginshikin ta a 1999, har ta kai shekaru 20 da kafuwa, a bisa tsarin bin dokar kotuna, sannan kuma jami’an sojojin kasar nan sun kasance a koda yaushe cikin shirin kare kasar nan.
Daga nan sai Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa babbar matsalar da ta fi addabar Najeriya, ba daga gwamnatin jiha ko tarayya ko wani yanki ba ne, sai dai kawai ita ce tunanin da ke cikin kan su tun can tuni cewa ta hanyar tarzoma da tashin hankali ne kawai za a iya kawo canji.
“Watau irin masu wannan makahon tunanin kawo canji a cikin tarzoma da yada kiyayya, idon su ya rufe, ba su kallon hanyoyin tattauna batutuwa misali a majalisu, sai dai su rika tunanin tashin hankali ne kadai hanya mafitar kawo canji a Najeriya.